Kamar kullum dai shafin TASKIRA na tafe da Tsokaci na musamman, inda ya ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma dan tattaunawa a kai.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin matsalolin da wasu ma’auratan ke fuskanta a kan `ya’yansu, musamman ta bangaren Sirikansu (kakannin yaran), ta yadda kakannin ke shawaba yaro, ta hana uwar yaro dukan danta ko da kuwa ya yi kuskuren da za a dake shi.
- “Akwai Masu Shekara 18 Zuwa 20 Ba Tare Da Hukunci Ba A Gidan Gyaran Hali Na Kuje”
- PDP Ta Nemi Buhari Da Ya Tilasta Wa ‘Yan APC Su Saki Sabbin Kudin Da Suka Boye Don Sayen Kuri’u
Da yawan wasu kakannin na hana kowa dukan jikansu komai tsananin laifin da yaro zai aikata, wanda dalilin dukan yaron wasu iyayen ke fuskantar mutuwar aure wajen mazajensu ko kuma karin aure, sakamakon kakar yaron ta ba wa danta umarnin hakan.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan matsala; Ko mece ce ribar yin hakan ko akasin hakan? Wacce irin matsala hakan za ta iya haifarwa? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki) daga Jihar Kano Nijeriya:
Gaskiya wannan matsalar tana ci min tuwo a kwarya, domin rashin daukar mataki na hukunci akan yara. Kuma idan an dake su kakanni ko iyayensu maza na jin zafi karshe har su raba aure tsakaninsu da mahaifansu. Hakika hakan yana matukar lalata makomar tarbiyyar al’ummar mu, domin kuwa mafiya yawan yaran da suka lalace wannan ne sila, Allah ya gyara mana Amin. Babu wata riba a cikin aikata hakan gaskiya, domin sai ka yarda ka hukunta naka sannan zai gyaru a cikin al’umma. Daga cikin matsalolin da hakan zai haifar su ne; Raini tsakanin yara da mahaifinsu, Rashin tarbiyya, Rashin girmama manya, Wulakanta sauran al’umma. Shawara ita ce; su daina aikata hakan, domin ba abu ne mai kyau ba. Fatan Allah ya gyara mana, ya kuma inganta rayuwar mu.
Sunana Zahra’u Sa’eed daga Jihar Kano:
Wasu iyayen suna yin hakan ne saboda kauna, kuma gaskiya wannan ba kauna bace, ya kan janyo lalacewar yara da dama za ka ga yaran ba me fada musu su ji. Akasin hakan na jawo lalacewar yaran da kuma rashin wadatacciyar tarbiyya ga yaran. Gaskiya zai iya haifar da matsaloli kamar ga ‘ya’ya mata rashin kamun kai, da kuma rashin zuwa makaranta, da kuma raina iyayen nasu mata, ga maza kuma shaye-shaye da sauransu. Gaskiya shawarata shi ne; iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu musamman ta hanyar tsawatarwa da kuma basu ilimi da tarbiyya ta hanyar nunawa kakanin nasu suna da mahimmaci
Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:
Wannan ba karamar Matsala ba ce, saboda tarbiyyar yaro wani lokacin dole sai an hada da duka, hana dukan zai iya haifar da lalacewar tarbiyyar ‘ya’yan. Babu riba kwata-kwata a hana bawa yaro cikakkiyar kulawa. Kwarai da gaske idan yaro ya tashi ba a kwabarsa zai Iya lalacewa ta fuskoki da dama kamar; Shaye-shaye, Sace-sace, Neman Mata, Fadace-fadace da sauransu. Iyayen yara su kula ba a kowanne laifi ake dukan yaro ba. Masu hana dukan su sani cewa ana dukan ne dan yaro ya gane yayi laifi, kuma su kansu iyayen da suke dukan ba dan su ji dadi suke yi ba, sai dan su ga yaro ya zama na gari me jin magana.
Sunana Mustapha Abdullah Abubakar daga Jihar Jos:
Da farko dai a nawa fahimtar sirikan da ba sa son a dakar musu jikokinsu ko da kuwa iyayen yaran ne, abin da ke saka hakan shi ne; Akwai shakuwa mai karfi ne tsakaninsu da jikokinsu, wanda matukar ana dukan jikokinsu sukan ji ba dadi, ko da kuwa iyayen yaran ne. A wani bangare kuwa, tun kafin Aure akan samu rashin fahimta tsakanin, uwar Ango da ita kanta Amaryan, wanda kan iya haifar da sirika ta tsani mahaifiyar yaro ko yarinyar, ta hanyoyi da dama. Wani lokacin sirikan kan fake da hakan ne domin tunzura uban yaro ya sake yin Aure, sabida rashin jituwar su. A Gaskiya babu wata riba ga duk sirikar da za ta saka danta sakin matarsa, ko kuma karo aure. Sabida wani dalili matukar ana so aci ribar aure. Akasin hakan ka sa ita uwar yaron daina ganin girman mahaifiyar mijin nata, akansin haka kuma kan haifar da munmunar matsala da rashin fahimta ko kuma kiyayya tsakanin bangarori guda biyu wato dangin Ango da kuma dangi Amarya. Hakan Kan haifar da daina ganin girman juna, kan haifar da daina bin umarnin sirikai, kan haifar da musayan kalamai maras dadi tsakanin juna. Shawara ga surikai masu aikata irin wannan su ji tsoran Allah, su sani cewa wanna ba addini bane, son zuciya ne, da kuma bin hanyar halaka. Domin ko bayan mutuwar su, su kan tafi su bar mummunar tsana, ko rashin fahimta ga ‘ya’yansu. Iyayen yaro kuwa su yi koyi da kyawawan halayya kamar; hakuri, da juriya, da nuna biyayya ga zaman aure, domin suna bin umarnin fiyayan halitta ne wato Annabi Muhammad (S.A.W), mutukar suka yi hakan ba shakka sakamakonsu na da girma a wajan Allah subhanahu wata’ala.
Sunana Amina Mu’awuya Mukhtar:
Gaskiya hakan ba karamin babban kuskure ba ne, sabida hakan ya kan haifar da babbar matsala ga tarbiyyar yara, domin kuwa za su taso ba sa ganin darajarar iyayen su, za su taso a fandare ba sa ganin daraja da girmama duk wani na gaba da su, sabida tun farko sun gina su akan rashin ganin daraja da kimar iyayen su, duk wanda kuwa ya taso akan wannan turba to tabbas! ko ya girma a haka zai gina rayuwar shi, dan haka wannan babbar matsala ce. Hakan ba shida wata riba, domin kuwa ruguza tarbiyya ne, akasin hakan kuwa shi ne gaba daya iyalan mutum za su ta so cikin rashin samun nagartacciyar tarbiyya. Tabbas! yana haifar da tarin matsaloli ba kadan ba. Rashin ganin darajar iyayen da suka haifi mutum, Gurbacewar tarbiyyar zuri’a. Shawarar da zan basu shi ne; ya kamata su gane cewa abin da suke ba dai-dai bane ko a cikin addinin musulunci, domin kuwa Manzon (s.a.w) ya ce; “Yardar Allah tana tare da Yardar iyaye, haka fushin Allah yana tare da fushin iyaye”, to ko dan wannan zan ce daga bakin mai gaskiya ya kamata ace Mutane mu hankalta mu bar jikokinmu su yi wa iyayen su biyayya, matukar biyayyar bata kaucewa umarnin Allah da Manzon sa ba, Allah ya sa mu dace.
Sunana Abdullahi Dahiru Matazu daga Jihar Katsina:
A Gaskiya wannan ba karamar matsala ba ce, domin idan muka yi duba da wasu abubuwan irin su; rashin ji na yaro, da kuma rashin yin sallah, wannan duk laifi ne da bai kamata a kyale yaro ba, dole a hukunta shi. Saboda haihuwar sa aka yi ba daga sama ya fado ba, kuma wannan ya tabbatar da cewa su fa sun tsufa babu abun da suke so illa yaran nan, saboda suna abokansu, kwakwalwar su iri daya ce. Babu wata riba sai ma faduwa, zai iya haifar da babbar matsala, kana zaune da matar ka lafiya an ce ka saketa, ka auro wata wacce baka san halinta ba. Kome iyayenmu za su yi mana ka da mu ji haushi, saboda su ne tsatson da aka samo mu jikinsu, mu yi ta hakuri da addu’a har Allah ya sa mu rabu lafiya.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Gaskiya hakan ba daidai bane, sakamakon hakan zai iya sa yaro ya zama ba shi da cikakkiyar tarbiyya, kuma baya ganin girman iyayansa. Yin hakan ba shi da wata riba, face rabuwar kai tsakanin ‘ya’ya da iyayan su, zai haifar da rashin ganin darajar iyayaye, sanan zai sa yaro ya gangare ya zama ba ya jin maganar kowa. Shawarata a nan ita ce; masu yin irin wannan ita ce su guji bata tarbiyyar jikokinsu, saboda gudun abin da zai je ya zo. Na gode, ina yi wa kowa fatan alkhairi.
Sunana Aisha Umar Kano:
Toh! gaskiya sirikan suna tunanin so ne suke nuna wa jikokin ba su san suna hallakar da rayuwarsu ba, ne Musamman idan suka sa aka saki iyayen yaran, ta nan ne yaran za su tashi ba tarbiyya, ba su ganin kimar kowa sun raina kowa saboda tun farko ba a tsawata musu ba.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Gaskiya hakan yana faruwa kuma wannan ba ita ce mafita ba, ya kamata kakanni su rinka sawa zuciyarsu hakuri akan kananun abubuwa irin wannan. Sannan su ma iyaye mata su yarda cewa duka ba shi ne mafita ba ga tarbiyyar yara, addu’a da nasiha da tsawatarwa ita ce mafita. Ba shi da wani riba ko alfanu, karshe ma ya kawo rabuwar aure ko rusa zamantakewa me dadi, on haka kawar da kai ya fi komai a garesu. Matsalolin sun hada da Rashin ganin girman surukan, saboda sawa a sake su. Yawaita mutuwar aure, Sawa jikoki su raina kakanninsu mata saboda sawa a saki iyayensu da suke yi. Shawara ita ce; Iyaye su rinka yin abin da za su gyara zamantakewar ‘ya’yansu, ba lalatawa ba. Iyaye mata su rage dukan kananan yara a matakin horo, kakanni su daina shiga lamarin ‘ya’ya da jikokinsu dan hakan na janyo raini da rashin zamantakewa.