Kamar kowanne mako shafin Taskira ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma ta fanni da dama. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin halin wasu mazan masu zuwa wajen budurwa da niyyar neman aure. Sai dai kuma mazan na boye wa ‘yan matan yawan ‘Ya’yan da suke da su, ko kuma girman ‘yar da suke da ita, tare da boye asalin garinsu ko makamancin haka, ba tare da yarinyar ko iyayen yarinyar sun sani ba, har sai lokacin da aure ya gabato tukunna su ji labari a wani waje, gaskiya ta bayyana, har kuma ta kai ga an fasa wannan aure. Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin matasa game da wannan batu; Ko mene ne amfanin hakan?, Ko me za a kira hakan da shi?, Me ya ke janyo hakan?, kuma ta wacce hanya za a magance afkuwar hakan?. Ga dai ra’ayoyin na su kamar haka:
Zahrau Abubakar (Dr Zarah) Karamar Hukumar Nasarawa Jihar Kano:
A gaskiya hakan bai da amfani rashin gaskiya ne da rashin Amana da zunzurutun yaudara, ai shi zaman aure ya wuce abin da za a gina shi akan karya, saboda zama ne da ake sa rai na har abada. So komai yawan yaranka ka sanar da wacce kake son aura ba komai bane idan tana sonka tsakanin ta da Allah babu ruwanta da yawan yaranka, bawai sai bayan aure ko kuma aure ya zo daf! ba ta sami labari a wani gun ba, gaskiya hakan bai dace ba. Wannan yaudara ce ta zahiri, Rashin gaskiya ne kuma cin Amana ne. A gaskiya abin da ke janyo hakan na farko rashin gaskiya, na biyu kuma may be shi mijin yana ganin in ya fadi hakan kamar ita amaryar ba za ta amince ba, ko za a zuga ta, ko kuma akasin hakan. Shawarar da zan bawa masu aikata irin wannan dabiar gaskiya ya kamata su ji tsoran Allah, su daina wannan ba hali na gari ba ne, bai kamata ake boye manya manyan abubuwa ba, saboda ni gani nake kana sona ina sonka mun yarda mun amince za mu zauna a inuwa guda to me zan boye?, wanda kuma nasan dole gaskiyar za ta fito wata rana, kuma daga nan girma da mutunci na duk ya zube a idanunsa. A gaskiya bai kamata ba ya kamata a rike amanar juna.
Mas’ud Saleh Dokatawa:
Abubuwan da ya sa yawancin mazaje ke boye gaskiyar su yayin neman aure, musamman idan suna da ‘ya mace babba ko wasu abubuwa makamantan haka shi ne, yaudara ce, karya ce, ha’inci ne, sannan wasu matan in aka gaya masu ba za su yarda ayi aure ba, saboda ra’ayinsu na kashin kansa. Don haka dole ne a samu rashin fahimtar juna. Yadda za a kira hakan shi ne yaudara da zambo cikin aminci. Abin da yake janyo hakan matan ba sa son auren mazajen da suke da yara, don kada su yi wa ‘ya’yan wata bauta, su kuma mazan sun kamu da sonsu sosai yadda sai sun boye gaskiya don samun auren. Hanyoyin da za a magance a rinka bayyana gaskiya a duk abin da za su yi na neman aure, su kuma matan su rage buri da kuma auren me ‘ya’ya. Shawara ita ce su ji tsoron Allah su daina, sannan kuma su kiyaye hakkokin addini da al’adar malam bahaushe da mu’amala ta musulunci.
Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:
Tsabar son rai ne da tunanin idan sun fadi gaskiya ba za su sami auren ba, shir me ne da shiririta. Ya kamata Mutum yayi gaskiya a neman Aurensa. Shawrats su ji tsoron Allah, su sani cewa duk Auren da aka gina shi akan karya baya karko, kuma da wuri ake samun matsala a zamantakewa.
Ibrahim Ismail Ibrahim daga Jogana Jihar Kano:
Gaskiya dai hausawa na cewa ramin karya kurarrre ne, komai za ka yi a rayuwa ka kamanta gaskiya sai rayuwa ta yi kyau, duk abin da aka dora shi a doran gaskiya ya fi karko, dan haka ba hali ne mai kyau ba. Kuma duk mai irin wannan halayar Allah ya bashi ikon gyarawa, karya ce ke jawo hakan. Ta yadda za a magance shi ne; Duk yadda mutum ya ke ya kamanta gaskiya a duk lokacin da ya tsinci kansa a irin wannan hali, shawara su daina wannan dabi’ar su ji tsoron Allah a duk lamurinsu.
Safiyya Mustapha Mu’az daga Gurin Gawa:
Hakan ba shi da wani amfani sabida karya ce, kuma karya ba aba ce me kyau ba, kuma duk auren da aka gina ta hanyar karya baya albarka, da farko ya yi mata karya ya yi wa iyayenta da ‘yan uwanta karya, wanda zai janyo su daina ganin girmansa tun farko gwara ya fada mata gaskiya cewar yana da iyali idan ta ga tana son sa to sai ta aure shi a hakan, idan ba ta san me ‘ya’ya kuma sai ya rabu da ita ya nemi wata, saboda ko da ace ya aureta a hakan to ba za su taba jin dadin zama da junansu ba sakamakon wannan karyar da yayi mata. Yaudara, karya, abin da ke janyo hakan shi ne burin da ‘yan mata suka daurawa kansu cewa ba sa son namiji me mata duk da addini bai haramta ba, amma su suna son haramtawa, kaucewa afkuwar hakan ‘yan mata a rage buri saboda mutum baya kaucewa kaddararsa idan Allah yayi me matar za ki aura to ba yadda za ki yi. Sannan Maza ma su ma su gyara, idan sun je neman aure zuwansu na farko ya zauna yayi mata bayanin ko shi waye da adadin Iyalan dake da shi idan ta ga tana sonsa a hakan yayi, idan kuma ba ta da ra’ayin aurensa sai su hakura da junansu tun kafin su yi nisa, kuma wannan ita ce hanya mafi sauki da za a rabu da irin wannan matsaltsalun. Shawarata a nan ita ce a daina karya,.domin karya babu kyau, kuma kowa ya san da hakan.
Mansur Usman Sufi, Sarkin Marubutan Yaki Jihar Kano:
Mas’alar karyar da samari ke yi wa ‘yan mata gaskiya abu ne maras kyau, domin hausawa na cewa ramin karya kurarre ne, mafi yawan su rashin tsoron Allah ne ke sanya su aikata hakan ko soyayyar budurwar da tsoron kar su rasa ta. Hakan gaskiya abun kunya ne da zubar da daraja. Hanyar da za a magance hakan sh ine ya kamata kowacce yarinya a zaunar da ita a bayyana mata hanyoyi da siffofin makaryaci, domin ta haka ne za su fahimci duk saurayin da ya zo neman aurensu kafin akai ga tura iyaye. Babu lokaci da na bayyana kadan daga cikin siffofin da ake gane makaryacin saurayi. Shawarar da zan basu ita ce su yi gaskiya duk abin da yake rabonsu a wajen Allah za su samu.
Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Mafi yawancin samari da ‘yan matan duk makaryata ne, kowa yana yi wa kowa karya shi ne matsalar da take faruwa. Hakan ya zama cin amana da zamba, abin da yake janyo haka ba a gina soyayyar akan tubalin gaskiya shiyasa. Shawarata a nan ita ce a cire son zuciya a ji tsoron Allah, kuma a rike amana na gode.