Fili na musamman wanda ya ke bawa kowa damar tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya ke ci masa tuwo a kwarya. Abba Abubakar Yakubu ya bayyana abin da ya ke damunsa cikin zuciya game da masu kwacen waya, inda ya fara da cewa:
Musa Sani Aliyu wanda aka fi sani da Musa Khan, ma’aikaci ne a gidan rediyon Jalla da ke birnin Kano. Watarana da daddare misalin karfe tara, a kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya tashi daga wajen aikinsa a daidai kan titin Club Road kusa da ofishin Kwastom, yayin da yake tafiya wasu batagari a kan babur suka sha gabansa yayin da suka nemi ya bada wayar da ke jikinsa, kafin ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihunsa, sai daya daga cikin su ya fitar da wata wuka da ke jikinsada aka yi wa kira ta musamman, ya sare shi a hannu. Zafin wannan saran ya sa Musa ya yi kuwwa domin neman taimako, ganin yadda jama’a suka fara nufowa wajen ya sa nan da nan barayin suka hau babur dinsu suka gudu. Ganin yadda jini ke zuba daga jikinsa inda suka sare shi sai aka garzaya da shi asibiti, domin ceto rayuwarsa. Musa Khan daya ne daga cikin daruruwan mutanen da suka tsallake rijiya da baya, yayin harin da ‘yan daba masu kwacen waya suka kai musu a lunguna da anguwanni daban daban na cikin birnin Kano, da sauran manyan biranen arewacin kasar nan.
Rahotannin da ke fitowa daga jihohi daban daban, irin su Kano, Kaduna, Katsina, Filato, Bauchi, Gombe, Adamawa da sauran birane da dama na bayyana cewa, ana samun munanan hare hare daga miyagun matasa wadanda shekarunsu ba su wuce 14 zuwa 25 ba, da ke dauke da muggan makamai kuma suke far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a kan tituna, da lunguna, har da cikin ababen hawa da gidaje, suna kwace musu wayoyinsu na hannu da wasu abubuwa da suka mallaka, wani lokaci ma an ce har ruwa mai guba na asid suke watsawa mutane, don jikkata su da yi musu lahani, har ma da kisan gilla.
A wasu lokutan wadannan matasa kan yi amfani da wuraren taruka kamar na siyasa, biki ko kuma idan an samu cinkoson ababen hawa a kan tituna sai su yi amfani da makami kamar wuka, adda, musilla, kaho, da wasu makamai masu ban tsoro, wajen yi wa mutane kwace. Yayin da suke wa mutane barazana a kan idan har basu bayar da abin da suke bukata ba sai sun yi musu rauni ko ma su hallaka su baki daya. Kuma abin takaici a yayin da suke wannan mummunar dabi’ar ba sa kyale yara, da mata, ballantana dattijai masu rauni.
Wasu daga cikin mazauna birnin Kano sun ce irin wannan kwace na waya ba wai na kan hanya kawai ake yi wa ba, a kan je har gida a yi sallama da mutum sannan a nemi ya bayar da wayarsa idan bai bayar ba sai a sa masa makami, a jikkata shi ko a kashe. Wasu rahotanni na bayyana cewa a kowacce rana a kalla mutane 15 ne suke gamuwa da ibtila’in sara da wuka ko wani makami ta dalilin kwacen waya a Jihar Kano. Yayin da a wata guda ake samun mutanen da tsautsayi ke fadawa kansu ta dalilin kwacen waya da yawan su ya kai 450. A daidai lokacin da nake wannan rubutu masu kwacen waya sun kashe mutane biyu cikin mako guda a Jos, ban da wadanda ake jikkatawa kusan a kowacce rana. Abin da yake kara daga hankalin masu fada a ji, da ke tattaunawa kan hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan matsala da ke neman gagarar jami’an tsaro da ‘yan banga, duk kuwa da kokarin da suke yi ba dare ba rana, don kama masu aikata irin wannan danyen aikin da gurfanar da su gaban kuliya.
Malam Nura Alhassan shi ne shugaban wata kungiyar matasa ta Jos Peace Banguard, wacce ke taimakawa wajen wayar da kan matasa masu harkar daba da shaye shaye, da canza musu tunanin su daga mummunar hanyar da suke kai, don su zama mutanen kirki kuma ‘yan kasa nagari. A wata ganawa da muka yi da shi ya bayyana min cewa, wannan matsala ta kwacen waya da ke dada ta’azzara na kara daga musu hankali sosai, musamman ganin a baya an samu saukin matsalar sakamakon kokarin da suka yi na hada kan kungiyoyin matasa ‘yan daba masu gaba da juna tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, inda aka sasanta su tare da kulla yarjejeniyar daina rikici a tsakaninsu, wanda sau da dama ke kaiwa ga kashe kashe da sare saren juna. Amma tun farkon wannan shekarar ta 2023, harkar fadan daba da kwacen waya ta sake kunno kai, musamman bayan dawowar harkokin siyasa.
Malam Nura ya ce, duk da yake jami’an tsaro na nasu kokarin amma ba za a nade hannu a sa musu ido ba, dole ne za su sake yunkurawa su ga sun gayyato tubabbun ‘yan daba da a baya suka yi ta fafutukar ceto su daga wannan mummunar hanya, domin amfani da su wajen zakulo kangararrun yaran da aka sani suna wannan abin da nufin zama da su don a dakile ci gaba da wannan mummunar halayya. Ya dora alhakin dawowar harkokin ‘yan daba da amfani da makamai da yara matasa ke yi kan wasu baragurbin ‘yan siyasa da ke sanya matasan cikin gurbatacciyar rayuwa ta shaye shaye da kai hari kan abokan adawa, a duk lokacin da kudaden da suka saba bai wa yaran ya kare ko suka dakatar da ba su, shi ne suke komawa fashi da makami, da kwacen wayoyi don su samu abin sayen kayan maye.