ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsokaci Kan Maza Masu Boye Bayanan Kansu Wurin Neman Aure

by Rabi'at Sidi Bala
3 years ago
Zahra'u Abubakar (Dr. Zarah)

Zahra'u Abubakar (Dr. Zarah)

Kamar kowanne mako shafin Taskira ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma ta fanni da dama. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin halin wasu mazan masu zuwa wajen budurwa da niyyar neman aure. Sai dai kuma mazan na boye wa ‘yan matan yawan ‘Ya’yan da suke da su, ko kuma girman ‘yar da suke da ita, tare da boye asalin garinsu ko makamancin haka, ba tare da yarinyar ko iyayen yarinyar sun sani ba, har sai lokacin da aure ya gabato tukunna su ji labari a wani waje, gaskiya ta bayyana, har kuma ta kai ga an fasa wannan aure. Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin matasa game da wannan batu; Ko mene ne amfanin hakan?, Ko me za a kira hakan da shi?, Me ya ke janyo hakan?, kuma ta wacce hanya za a magance afkuwar hakan?. Ga dai ra’ayoyin na su kamar haka:

Zahrau Abubakar (Dr Zarah) Karamar Hukumar Nasarawa Jihar Kano:

Tsokaci
Zahra’u Abubakar (Dr. Zarah)

A gaskiya hakan bai da amfani rashin gaskiya ne da rashin Amana da zunzurutun yaudara, ai shi zaman aure ya wuce abin da za a gina shi akan karya, saboda zama ne da ake sa rai na har abada. So komai yawan yaranka ka sanar da wacce kake son aura ba komai bane idan tana sonka tsakanin ta da Allah babu ruwanta da yawan yaranka, bawai sai bayan aure ko kuma aure ya zo daf! ba ta sami labari a wani gun ba, gaskiya hakan bai dace ba. Wannan yaudara ce ta zahiri, Rashin gaskiya ne kuma cin Amana ne. A gaskiya abin da ke janyo hakan na farko rashin gaskiya, na biyu kuma may be shi mijin yana ganin in ya fadi hakan kamar ita amaryar ba za ta amince ba, ko za a zuga ta, ko kuma akasin hakan. Shawarar da zan bawa masu aikata irin wannan dabiar gaskiya ya kamata su ji tsoran Allah, su daina wannan ba hali na gari ba ne, bai kamata ake boye manya manyan abubuwa ba, saboda ni gani nake kana sona ina sonka mun yarda mun amince za mu zauna a inuwa guda to me zan boye?, wanda kuma nasan dole gaskiyar za ta fito wata rana, kuma daga nan girma da mutunci na duk ya zube a idanunsa. A gaskiya bai kamata ba ya kamata a rike amanar juna.

ADVERTISEMENT

Mas’ud Saleh Dokatawa:

Tsokaci
Mas’ud Sale Dokatawa

Abubuwan da ya sa yawancin mazaje ke boye gaskiyar su yayin neman aure, musamman idan suna da ‘ya mace babba ko wasu abubuwa makamantan haka shi ne, yaudara ce, karya ce, ha’inci ne, sannan wasu matan in aka gaya masu ba za su yarda ayi aure ba, saboda ra’ayinsu na kashin kansa. Don haka dole ne a samu rashin fahimtar juna. Yadda za a kira hakan shi ne yaudara da zambo cikin aminci. Abin da yake janyo hakan matan ba sa son auren mazajen da suke da yara, don kada su yi wa ‘ya’yan wata bauta, su kuma mazan sun kamu da sonsu sosai yadda sai sun boye gaskiya don samun auren. Hanyoyin da za a magance a rinka bayyana gaskiya a duk abin da za su yi  na neman aure, su kuma matan su rage buri da kuma auren me ‘ya’ya. Shawara ita ce su ji tsoron Allah su daina, sannan kuma su kiyaye hakkokin addini da al’adar malam bahaushe da mu’amala ta musulunci.

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:

Tsokaci
Musbahu Muhammad

Tsabar son rai ne da tunanin idan sun fadi gaskiya ba za su sami auren ba, shir me ne da shiririta. Ya kamata Mutum yayi gaskiya a neman Aurensa. Shawrats su ji tsoron Allah, su sani cewa duk Auren da aka gina shi akan karya baya karko, kuma da wuri ake samun matsala a zamantakewa.

Ibrahim Ismail Ibrahim daga Jogana Jihar Kano:

Tsokaci
Ibrahim Isma’il Ibrahim

Gaskiya dai hausawa na cewa ramin karya kurarrre ne, komai za ka yi a rayuwa ka kamanta gaskiya sai rayuwa ta yi kyau, duk abin da aka dora shi a doran gaskiya ya fi karko, dan haka ba hali ne mai kyau ba. Kuma duk mai irin wannan halayar Allah ya bashi ikon gyarawa, karya ce ke jawo hakan. Ta yadda za a magance shi ne; Duk yadda mutum ya ke ya kamanta gaskiya a duk lokacin da ya tsinci kansa a irin wannan hali, shawara su daina wannan dabi’ar su ji tsoron Allah a duk lamurinsu.

Safiyya Mustapha Mu’az  daga Gurin Gawa:

Tsokaci
Safiyya Mustapha Mu’az

Hakan ba shi da wani amfani sabida karya ce, kuma karya ba aba ce me kyau ba, kuma duk auren da aka gina ta hanyar karya baya albarka, da farko ya yi mata karya ya yi wa iyayenta da ‘yan uwanta karya, wanda zai janyo su daina ganin girmansa tun farko gwara ya fada mata gaskiya cewar yana da iyali idan ta ga tana son sa to sai ta aure shi a hakan, idan ba ta san me ‘ya’ya kuma sai ya rabu da ita ya nemi wata, saboda ko da ace ya aureta a hakan to ba za su taba jin dadin zama da junansu ba sakamakon wannan karyar da yayi mata. Yaudara, karya, abin da ke janyo hakan shi ne burin da ‘yan mata suka daurawa kansu cewa ba sa son namiji me mata duk da addini bai haramta ba, amma su suna son haramtawa, kaucewa afkuwar hakan ‘yan mata a rage buri saboda mutum baya kaucewa kaddararsa idan Allah yayi me matar za ki aura to ba yadda za ki yi. Sannan Maza ma su ma su gyara, idan sun je neman aure zuwansu na farko ya zauna yayi mata bayanin ko shi waye da adadin Iyalan dake da shi idan ta ga tana sonsa a hakan yayi, idan kuma ba ta da ra’ayin aurensa sai su hakura da junansu tun kafin su yi nisa, kuma wannan ita ce hanya mafi sauki da za a rabu da irin wannan matsaltsalun. Shawarata a nan ita ce a daina karya,.domin karya babu kyau, kuma kowa ya san da hakan.

Mansur Usman Sufi, Sarkin Marubutan Yaki Jihar Kano:

Mas’alar karyar da samari ke yi wa ‘yan mata gaskiya abu ne maras kyau, domin hausawa na cewa ramin karya kurarre ne, mafi yawan su rashin tsoron Allah ne ke sanya su aikata hakan ko soyayyar budurwar da tsoron kar su rasa ta. Hakan gaskiya abun kunya ne da zubar da daraja. Hanyar da za a magance hakan sh ine ya kamata kowacce yarinya a zaunar da ita a bayyana mata hanyoyi da siffofin makaryaci, domin ta haka ne za su fahimci duk saurayin da ya zo neman aurensu kafin akai ga tura iyaye. Babu lokaci da na bayyana kadan daga cikin siffofin da ake gane makaryacin saurayi. Shawarar da zan basu ita ce su yi gaskiya duk abin da yake rabonsu a wajen Allah za su samu.

Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:

Tsokaci
Abubakar Muhammad Sheshu

Mafi yawancin samari da ‘yan matan duk makaryata ne, kowa yana yi wa kowa karya shi ne matsalar da take faruwa. Hakan ya zama cin amana da zamba, abin da yake janyo haka ba a gina soyayyar akan tubalin gaskiya shiyasa. Shawarata a nan ita ce a cire son zuciya a ji tsoron Allah, kuma a rike amana na gode.

Tsokaci
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
Hakkinmu Ne Mu Kawo Karshen Masu Kwacen Waya (I)

Hakkinmu Ne Mu Kawo Karshen Masu Kwacen Waya (I)

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.