• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

by Rabi'at Sidi Bala
5 months ago

Kamar dai kowane mako shafin TASKIRA na zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu matasa ke dauko wa kansu aure ba tare da sun shirya ba, duba da irin wasu matsalolin da ake samu a wasu wuraren wanda kuma asalin faruwarsu dalilin rashin sana’a ne.

  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz
  • Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai

Wasu matasan sukan tattagowa kansu aure alhalin ba su da wata kwakkwarar sana’a sai kame-kame, wasu ma a fannin karatun boko iya sakandare kawai suka tsaya ba tare da wani rashi ba. Yayin da iyaye suka hana yin auren har sai yaro ya karasa karatu ko ya samu cikakkiyar sana’a, wasu daga cikin matasan sukan bujirewa iyayen har ta kai ga sun yi rashin kunya cewar; ba wanda ya isa ya hana auren, tare da fadin cewa; za su zauna ko a gidan haya ne, watarana Allah zai hore. Ta bangaren matan ma wasu na bayar da gudunmawarsu tare da taka rawar gani wajen goyon bayan auren matashin da ba shi da kwakkwarar sana’ar, domin kuwa wasu daga ciki har kwantawa jinya suke sakamakon hana yin auren, har sai iyayen sun amince sannan su warke. Abu dubawa a nan shi ne; matasan kanana ne sosai ta yadda suke da lokacin neman ilimi da kuma fafutukar samun sana’a mai karfi tun kan lokaci ya kure musu.

Dalilin hakan ya sa muka ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin TASKIRA game da wannan batu; Me za a ce akan hakan?, Ko akwai wasu matsaloli da ka iya afkuwa ga su matasan yayin da suka yi aure babu wata kwakkwarar sana’a ko wani ilimi da zai amfanar a gaba?, Fadi amfanin yin aure tare da kwakkwarar sana’a ko ilimin zamani, wanda aka sani.

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

LABARAI MASU NASABA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:

Abin da ma yake faruwa kenan yanzu wallahi matasan nan maza! namiji babu sana’a babu isasshen ilimin zamani ke wallahi na addini ma wani babu sai ya tattago aure ko da yake an ce adashi suke shiga da an dauka sai zancen kai kudi karshe dai abar iyaye da wahala shi ya sa auren ma baya cin Litinin da Laraba an watse. Abin cewa nan yaro dai ya nutsu ya nemi sana’a da zai dogara da kansa sannan ya iya daukar nauyin iyali kuma a nemi karatu bakin iyawa. Su iyaye suna gujewa yaro abin da zai je ya zo ne ka dauko ‘yar mutane babu sana’a za a ci soyayya ne ina kai ba karatu ba sai kame-kame wani lokacin ma su iyaye su yaro yake bari da wahala a ci da shi a ci da matarsa, in Allah ya kawo rabo haka za a yi ta kin an haihu ko rigar jariri ba a siya ba. To, duk namijin da yake da kwakkwarar sana’a ai shi ne namijin aure babu rashin ci bale rashin sha da sutura, ya yi wa kansa ya yi wa iyali ya yi wa iyayen bakidaya.

Sunana Lubabatu Auta Ingawa:

A gaskiya akwai kuskure me girma da kuma da-na-sanin da yake biyo bayan yin aure babu sana’a da kuma karancin ilimi. Babban kalubalen shi ne; rashin iya sauke nauyin duk wata dawainiya ta matar saboda babu wata sana’a ko aikin yi ga mijin da kudi zai iya shigo masa. Matasa masu son aure ina baku shawara ku tabbatar da kuna da abin yi wanda zai iya rike gida dan gudun je-ka-nayi-ka, idan an taru an yi maka aure ba fa za a taru wajen rika maka mata ba. Sannan ina kira ga iyaye su jajirce wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ayyukan yi ko sana’o’i da kasuwanci kafin aure. Ke ma da za a aura kada ki bari soyayya ta debe ki, ki amince da auren ci-ma-zaune, wallahi idan ta kakare mafitar kawai shi ne saki, ki dawo gida ki zama karamar bazawara. A rika hakuri da jiran lokaci da tunani me kyau kafin aiwatar da komai na rayuwa.

 

Sunana Murjanatu Nasir daga Naija:

Wannan kuskure ne babba daukowa kai aure ba tare da sana’a ba, ina ganin kokarin masu yin hakan, na gaishe ku ‘yan kunar bakin wake, wannan ai sakawa kai damuwa da kuma nemawa kai rashin kwanciyar hankali ne bayan an yi aure. Dalilai na kuwa su ne; muddin aka yi aure tun kan soyayya ta kare za a fara fuskantar matsaloli da kalubalen da aka ja wa kai, rashin abubuwa zai yi sallama sakamakon masu taimakawar sun fara gajiya to, babu sana’a sai roko, karantun ma wani ba yadda ba a yi ba ya samu ya karasa ko takaddunsa ya ajjiye watarana a dace amma mutum ya ki sabida zuciya ta afka tafkin kogin soyayya. Roko zai yawaita yayin da ta haihu roko zai ci gaba, kai ne nan, gobe kai ne can kullum cikin roko, tun ana baka har a daina bakai, wani in ya ji tausayinka ya ce ka kawo takaddunka ya sama maka aiki nan ma babu su, har girma ya zo karfi ya kare.

 

Sunana Hassana Sulaiman Hadejia A Jihar Jigawa:

Wasu daga cikin matasan abin da ke sa su yi hakan shi ne gasa da take shiga tsakaninsu na cewa wane yayi ni ma ko ta ya sai nayi auren. Kuskuren da yake tsakaninsu matasan da kuma su kansu iyayen shi ne rashin tunanin mai hakan zai iya janyo wa gaba, kawai suna yanke hukuncin cewa idan aka yi Allah ne zai hore. Tabbas akwai matsalolin da za su iya zuwa gaba kamar; rashin zaman lafiya da samun nutsawa cikin zamantakewar auren kansa, da yawaitar samun matsalolin da za su iya haifar da rabuwar auren kansa. Yin aure da kyakkyawar sana’a yana haifar da gobe mai kyau ga zamantakewar aure, da kuma hasashen samun nutsawa da samar da tarbiyyar yara idan an samu. Shawarar da ya kamata kowanne bangare ya dauka a nan shi ne; Auren lokaci ne kuma idan yayi kowa zai yi kawai dai ana dan zurfafa tunani kafin yin nasa.

 

Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jahar Jigawa:

A gaskiyar magana wasu matasan sukan bijirowa kansu aure alhalin basu da halin yi amma kuma ni a ganina laifin iyayen su ne saboda a karkara ma iyayen su ne suke daure musu gindi tunda ciyarwar ma iyayen su ne suke yi ba wai matasan ba. Haka zalika dukka buyin suna kuskure mai makon a daurewa matashi gindi yayi sana’a ko karatu mai zurfi sai kawai daya fara tasawa sai ayi masa aure kuma dole ana samun rabuwar aure barkatai saboda bashi da ilimin auren. Akwai matsala ana samun rabuwar aure barkatai, ma’auratan basa samun jittuwa. Amfani yin aure da kwakkawar sana’a shi ne matshin zai iya rike matar da duk wata dawainiyar ta tazaman aure. Shawarar ita ce matashi ya dage da neman sana a da kuma ilimin sannan iyayen su ma suna nusar da yaransu akan neman sana’a da kuma ilimin.

 

Sunana Fatima Nura Kila A Jihar Jigawa:

Tabbas hakan babban kuskurene a gare mu yin aure ba sana’a, ya kamata mu matasa mu nutsu mu san me muke yi domin matukar ba sana’a aka yi aure, auren ba inda zai je zai rabu saboda babu kulawa ta fannin addininmu daya tanadar. A wannan bangaren gaskiya daga matan har mazan ba ma kan daidai akan wannnan abun, domin kuwa sana’a babbar jigo ce daga mazan har matan. Tabbas akwai sun hada da; Yawan tunani, zaman banza, saurin fushi, sata da sauransu. Tabbas amfanin shi ne; samun nutsuwa da cikar buri da kuma samun lafiya. Ya kamata mu matasa mu tashi mu nemin sana’a idan muka tsaya da kafafunmu sai mu yi aure domin bahaushe ya ce babu maraya sai rago. Iyaye kuma su ci gaba da tsayawa akan ‘ya’yansu wajen ganin sun inganta rayuwar ‘ya’yansu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu
Taskira

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Kishi
Taskira

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

October 12, 2025
Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu
Taskira

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

October 4, 2025
Next Post
CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari

CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari

LABARAI MASU NASABA

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai

Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai

October 26, 2025
El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu

October 26, 2025
Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.