ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tubabben Kwamandan Boko Haram Ya Bayyana Ta’asar Da Suka Tafka A Sambisa

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
Boko

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

An Kama Sojoji Biyu A Legas Kan Alaka Da Sarrafa Magungunan Jabu

ADVERTISEMENT

Wasu daga cikin tsofaffin kwamandojin kungiyar Jama’atu Ahlussunnah lil’da’wati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram sun bayyana nadamar irin ta’addancin da suka tafka a matsayinsu na mayakan kungiyar a baya.

Da suke tattaunawa da sashen Hausa na Muryar Amurka, daya daga cikin hadiman dake zama daya daga cikin hadiman tsohon shugaban kungiyar Abubakar Shekau, kuma daya daga cikin wadanda suka sace daliban Chibok, ya ce abin da suka yi a baya hakika bai dace ba, kuma babban abin takaici ne.

  • Mukalar Shugaba Xi: Hakika Kasar Sin Ba Ta Yi Wa Duniya Rowar Kaifin Basirarta Ba
  • Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 5.7 A Watanni Hudu Na Farkon Bana

Ya ce ya san Abubakar Shekau shekaru da dama kafin ma a fara rikicin na Arewa  maso Gabas, ko da aka ji wa shekau din rauni, an kawo shi Damaturu, inda yake jinya kuma a lokacin shike yi masa ‘yan aikace-aikace da wanki da da sauransu.

Bayan da kuma Shekau ya koma daji su kan aika masa da kudi don biyan bukatun yau da kullum kafin daga bisani shima ya bisu dajin, inda bayan samun horo, shima ya zama cikakken kwamandan dake jagorantar kai hare- hare.

Wannan tsohon kwamandan da ya ce ya jagoranci kai hare-hare a sassan Arewa maso Gabas da dama, ya yi ikirarin kashe fararen hula da sojojin da bai san adadinsu ba, al’amarin kuma da ya ce yana matukar bakin cikin hakan.

Bugu da kari, ya kuma yi bayanin yadda ya taka rawa yayin sace daliban Chibok inda suka kai su dajin Sambisa, koda yake ya ce shi bai auri ko daya ba, amma abokansa da dama sun aure su.

Ya ce babban abin da ya sa ya fice daga kungiyar ta’addancin shi ne yadda ake sa su karkashe mutane wasu ma ta hanyar yankan rago ba gaira ba dalili.

Da kuma yake amsa tambayar ko ina Leah Sheribu take? daliba zaya tilo daga cikin daliban Dapchi da ta rage a hanun yan ta’addan, wannan tubabben kwamandan na Boko Haram ya ce LEAH tana hanun mayakan Boko Haram tsagin ISWAP a yankin tafkin Tchadi.

Ya ce abokansu ne ke rike da ita, kuma sun mata aure har ta haifi yara biyu, namiji da mace, koda yake mijinta na farko ya rasu, amma wani dan ta’addan ya sake aure ta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
An Kama Sojoji Biyu A Legas Kan Alaka Da Sarrafa Magungunan Jabu
Kotu Da Ɗansanda

An Kama Sojoji Biyu A Legas Kan Alaka Da Sarrafa Magungunan Jabu

December 20, 2025
An Ceto Wasu Samari 11 ‘Yan Jihar Jigawa Daga Hannun Masu Fataucin Mutane
Kotu Da Ɗansanda

An Ceto Wasu Samari 11 ‘Yan Jihar Jigawa Daga Hannun Masu Fataucin Mutane

December 20, 2025
Next Post
Kotu Ta Aike Da Ramlat Princess Zuwa Gidan Gyaran Hali Na Kano Tsawon Watanni Bakwai

Gwamnatin Kano Ta Biya Wa Ɗalibai 1,740 Kuɗin Makaranta A Jami'ar Ilimi Ta Sa'adatu Rimi

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.