• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tufka Da Warwarar Akidar Kwankwasiyya

by Muktar Anwar
1 year ago
in Hannunka-Mai-Sanda
0
Tufka Da Warwarar Akidar Kwankwasiyya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwankwasiyya ce akidar ayarin wasu mutane da ake kira da Kwankwasawa a Jihar Kano da kewaye (kamar yadda wani mawakinsu, Gandu ke fadi) a siyasance, wadanda suka yi karfi tare da habaka a zangon mulkin Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na biyu, a matsayin gwamnan Kano, a Shekarar 2015—2019. Amma cikin zangon mulkin Kwankwaso na farko, daga Shekarar 1999 zuwa 2003, za a iya cewa tambari ko taken Kwankwasiyya da Kwankwasawa bai fara tashi, bugawa ko shahara ba irin yanzu.

Kalmar kwankwasiyya da kwankwasawa, na samun fassare-fassare iri-iri daga jama’ar Kano da wasunsu, bisa dogaro da wasu hujjoji na zahiri da ke faruwa a siyasar Kanon da ake mata take da sai dan Kano. A wajen mabiyin mazhabar siyasar kwankwasiyya a yau, kwankwasiyya na nufin “bin tunanin Kwankwaso da umarninsa a siyasance sau da kafa, ba tare da yin sanya ko neman wata hujja daga Madugun (Kwankwaso) ba, haka ne tsantsar akidar ta kwankwasiyya”. Ma’ana, duk abinda Madugu Kwankwaso ya ce a yi a siyasance, dole shi ne za a yi, batun ya gabatarwa da mabiyansa hujjar aikata wannan abu kuwa, samsam bai ma taso ba. Sannan, suna ma fassara aiyukan Kwankwason da kwankwasiyya.

  • Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Gaskiya Ta Bayyana Kan Bullar Mata Masu Shan Jini
  • Yadda Muka Yi Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Iyalina – Sarkin Kagarko

Da mutum zai nazarci wakoki da kuma furuce-furucen Kwankwasawa a Kano musamman, zai ji da bakinsu suna fadin cewa, “su makafi ne (cikin lamarin yi wa Kwankwaso biyaiya), ba su ganin kowa sai dan Musa (Kwankwaso)”. An ma ji wasunsu (ba dukansu ba) a kafafen sada zumunta na zamani na cewa, da Madugun nasu zai bar addinin musulunci, to fa suma a shirye ne suke da su yi ridda, su kauracewa addinin kacokan, saboda tsantsar kimar Kwankwason a wajensu, duk da cewa, ba a san hujjar da suka dogara da ita ba, tun da an ce ILIMI KOGI NE!

A wannan rubutu, ba a na nufin yin fashin baki ne ba game da rabe-raben zugar Kwankwasawa a Kano da kewaye, kawai dai za a dan ce wani abu ne game da inda ake samun tufka da warwara cikin akidar tasu ta kwankwasiyya, daga babban jagoransu Kwankwaso. Mene ne akidar kwankwasiyya?. “Aikace-aikacen Kwankwaso da kuma umarninsa a siyasance, a lokacin da yake bisa kujerar gwamnan Kano da akasin haka, shi ne ake nufi da akidar kwankwasiyya”. Bugu da kari, shi Kwankwason a kankin kansa, shi ne ma akidar da kwankwasiyya kacokan, tun da a wajen Bakwankwashen, mara baya ga duk wani motsi na Kwankwaso a siyasance, shi ne cikar mutum dan mazhabar siyasar kwankwasiyya na-gidi.

Da mutum zai dubi marigayi Malam Aminu Kano ya kira shi da shi ne ma “Tabo” a fagen siyasar Kano da kewaye, ai bai yi karya ba! Da kuma za a kalli marigayi Abubakar Rimi a ce shi ne ma “Santsi” bakidaya a fagen siyasar Kano da makota, nan ma ai ba a yi karya ba!. Ai Imamu Malik ne Malikiyyar bakidayanta, inda shi ma Imamu Shafi’i ya ciri tutar zama Shafi’iyyar kanta. Haka lamarin yake ga jerin Imaman mazhabobin addini da sauran kungiyoyin addini da waninsu. A daya bangaren, ai Mamman (Muhammad)Yusuf ne tozon Boko Haram a arewa maso gabashin wannan Kasa, haka cikin Shekarun 1980s a Kano, an fahimci Mamman (Muhammad) Marwa ne tatsinanci tsagwaronsa! Gwari-gwari, Kwankwaso ne Kwankwasiyya a cikin Kano da kewaye. Hatta cikin Alkur’ani akan kira ko fassara mutum da aiki, “…Shi Aiki Ne Ba Na Kwarai Ba (inda Allah ke wassafa dan Annabi Nuhu AS da mummunan aiki tsagwaronsa)”.

Labarai Masu Nasaba

Illar Raba Kan Mata

Fiye da Mata 50 Masu Haƙar Ma’adinai Sun Fuskanci Cin Zarafi a Jihar Nasarawa

Tufka Da Warwara Cikin Akidar Kwankwasiyya

Da fatan yanzu mai karatu ya fahimta cewa, za a iya fassara ko kiran Madugun Kwankwasiyyar da tsantsar akidar ta kwankwasiyya. Ta ina ne aka sami tufka da warwarar cikin akidar ta kwankwasiyya?. Shin, dan Kwankwasiyya ya gamsu da cewa, aikace-aikacen Kwankwaso a gwamnati, shi ma za a iya kiransa da kwankwasiyya? Duk da cewa, mai karatu bai ga amsar da suka ba da ba a nan, amma na tabbatar da cewa, babu wata cikakkiyar ma’anar Kwankwasiyya da wani Bakwankwashe ke tinkaho da ita, sama da aiyukan na Kwankwaso, musamman wadanda ya gabatar a lokacin da yake kan karagar mulki. Da irin wadannan aiyuka ne ma suke kafa hujjar cancantar yi masa makauniyar biyaiya sarmadan a fagen siyasa dari bisa dari (100%).

Idan mutum ya dauko aikace-aikacen na Kwankwaso lokacin da yake mulkar jihar Kano, kana ya dauko wani littafi ko a ce wani daftari da ya rubuta a matsayin “MANUFOFINSA”, lokacin da ya fito neman takarar kujerar shugaban Kasa cikin Shekarar 2023 karkashin inuwar jam’iyyar NNPP, mai suna, “My Pledges To You, 2022” (ma’ana, kyawawan manufofi da alkawurana ga “yan ), anan ne zai ga tufka da warwarar jibge iya ganinsa cikin akidar ta kwankwasiyya!!!.

A shafi na hudu (4) na wancan daftari da ke kunshe da manufofin Kwankwasiyya (My Pledges To You, 2022), madugu Kwankwaso ya ce, “…Babu shakka, za mu tsame “yan  daga cikin ramin talauci da suka jima da afkawa, ta hanyar zuwa da wasu tsararrun dabaru na rage radadi da  kashe kaifin talauci da suke ciki, inda za mu tabbatar cewa, iyalai da talauci ya kassara, sun kai ga matakin fin-karfin abinda za su ci, sutura…(da sauran bukatun rayuwa na yau da kullum)”.

Tufka Da Warwarar Akidar Kwankwasiyya

Don Allah jama’a, ta yaya ne ma, wanda ya zama silar kange kudaden Kananan Hukumomi 44 a Kano lokacin da yake gwamna, kuma wai yanzu yake fadin zai zo da wani sahihin shiri na tsame al’uma daga radadin fatara da talauci?. Gabanin Kwankwaso ya sunnanta yin garkuwa da kudaden kananan hukumomi a Kano, duk mutumin da ke zaune a jihar, ya kwana da sanin irin yadda mamakon arziki ke gudana a daukacin sako da lungu na jihar.

A wancan lokaci gabanin wawashe kudaden na kananan hukumomi da gwamnatin masu jan-kai suka yi a Kano, da daman shugabannin kananan hukumomi, na daukar wasu nauyaye-nauyayen da ke bisa wuyayen iyalai matalauta, misali, da yawa daga kananan hukumomin, na kai makudan miliyoyin kudade zuwa wasu jerin asibitoci a Kano duk karshen watan Duniya, don yin tiyata ko sayen wasu magunguna masu gayar tsada ga al’umomi marasa galihu da suka je asibitocin don neman lafiya, alhali ba su da fus.

Ciyaman na karamar hukumar Dala na wancan lokaci, Hon. Mahmoud Sani Madakin Gini, gabanin baiyanar akidar Kwankwasiyya bisa kujerar mulkin Kano a karo na biyu, na tura madudan kudade zuwa ga wasu da daman asibitoci a Kano irin su asibitin Murtala Mohd, Malam Aminu Kano, Air force, Waziri Gidado, Asibitin Kashi na Dala da sauransu, don biya wa raunanan iyalai da sauran jama’a abubuwan da suka gaza daukar nauyin kansu a harkar ta lafiya. Idan ka je karamar hukumar Nassarawa karkashin mulkin Hon. Nasiru Yusuf Gawuna da sauransu, suma suna yin irin wannan dawainiya da Hon. Mamuda Sani ke yi a karamar hukumar Dala.

Gabanin yin turkoko da gwamnatin Kwankwasiyya ta gadar tattare da asusun kananan hukumomi a Kano, za a iske ba ma wai gwamnatin jiha (karkashin Malam Ibrahim Shekarau) ba, kananan hukumomi na aikewa da dubban matasa zuwa ga Cibiyoyin Koyar da Sana’o’i iri-iri a Kano. Saboda haka sai aka zauna lafiya cikin lumana, kasantuwar dubban matasa na samun dubban gurabun aiyuka a ciki da wajen kananan hukumomin nasu.

Waccan dama ta sarrafa kudaden na kananan hukumomi da Ciyamomi ke da shi, sai aka wayigari matasa na kin karbar dubban takardun aikin gwamnati (ofa) a Kano. Ga jari, ga daukar nauyin jama’a a asibitoci, ga mamakon tallafin noma da ma na wata annoba idan ta samu, misali, ta’adin ruwan sama, mutum ya je ya ga irin dubban bahunan siminti, dubban kwanukan rufi hadi da tallafin makudan kudade da kananan hukumomi ke bai wa jama’arsu da irin waccan annoba ta rutsa da su. Kananan hukumomi su tallafa, ita ma gwamnatin jiha ta tallafa. Daga lokacin da gwamnatin Kwankwasiyya ta fara handame biliyoyin kudaden kananan hukumomin, sai aka wayigari irin wadancan tagomashi na alheri suka fara zama tarihi a tsakanin jama’ar Kano.

Daga lokacin da gwamnatin Kwankwasiyya a Kano ta tasamma yin mi’ara koma baya da hakkuna ko kudaden kananan hukumomi, na daga silar da ta kara rura wutar ta’addanci a wannan Kasa kamar yadda masana ke fadi, hatta mu ma a nan Kano, lokacin gwamnatin Kwankwasiyyar ne “yan-ta’adda suka fara kawo farmaki cikin jihar, wanda ya jaza macewar dubban mutane a Kanon. Irin wadancan hare-hare na ta’addancin ne ma suka kusa  jaza yin ajalin marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, sakamakon wuta da “yan ta’addar suka budewa ayarin Sarkin a unguwar Tukuntawa daura da Gidan Zoo na Kano.

Sakamakon datse lalitar kananan hukumomi da gwamnatin Kwankwasiyyar ta yi a Kano tsakanin Shekarun 2011 zuwa 2015, sai ya zamana irin wadancan makudan miliyoyin kudade na tallafi da gwamnatocin kananan hukumomi ke kai wa mabanbantan asibitoci a Kanon ya tsaya cik!. Batun yaye matasa daga koyon sana’o’i akai akai ya yi kasa wanwar, sai dan abinda ba a rasa ba. Sai jama’a suka koma yin barar neman tallafin kudaden da ba su kai sun kawo ba a kafafen yada labarai na Kano. Mata kan je bara da maular kudaden da ba su kere naira dubu goma (N10,000) ba a gidan rediyon, don ceto rayuwar danta ko ta mijinta da ke can kwance rai a hannun Allah cikin irin wadancan asibitoci da a lokutan baya ake kashewa talaka miliyan daya zuwa uku (N1,000,000) -(N3,000,000) daga lalitar karamar hukuma. Wai kuma irin wannan akida ta Kwankwasiyya da ta afkar da jama’ar Kano cikin wannan kangi, ita ce kuma yau take da bakin maganar za ta tsamo su daga talauci!!!. Ke nan, batun karya tattalin arzikin jama’ar Kano, tuni ya zama jini da tsoka a tsakanin rai, cikin zugar Kwankwasawan. Ko mai karatu ya manta dukiyar “yan kasuwar jihar ta Kano ta kusan naira miliyan dubu dari uku (N300, 000, 000, 000, 000, 00k) da gwamnatin kwankwasawan ta salwantar cikin kwanaki biyar kacal a Kano cikin wannan Shekara ta 2023?

 

In Sha Allahu A Mako Maizuwa Za A Dora.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Tasirin Sauyin Yanayi Ke Shafar Yankuna A Jihar Yobe

Next Post

Dalilai 20 Da Ke Sa Dalibai Faduwa Jarrabawa (1)

Related

Illar Raba Kan Mata
Hannunka-Mai-Sanda

Illar Raba Kan Mata

4 months ago
Fiye da Mata 50 Masu Haƙar Ma’adinai Sun Fuskanci Cin Zarafi a Jihar Nasarawa
Hannunka-Mai-Sanda

Fiye da Mata 50 Masu Haƙar Ma’adinai Sun Fuskanci Cin Zarafi a Jihar Nasarawa

10 months ago
Next Post
Dalilai 20 Da Ke Sa Dalibai Faduwa Jarrabawa (1)

Dalilai 20 Da Ke Sa Dalibai Faduwa Jarrabawa (1)

LABARAI MASU NASABA

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 13, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

May 13, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.