Rukayya Usman matashiya ce wacce take da himma tun tana karama, tana da matukar son ta ga ta zama ‘yar kasuwa, domin a ranta ba ta so ta ga mutane suna zaman banza ba tare da suna yin sana’o’i ko wasu ayyuka da za su amfani rayuwarsu ta hanyar samun kwabo da dari ba. Hakan ya sa ta yi tsayin daka domin ganin itama ta tsaya da kafarta wajen ganin ta kafa kasuwanci nata na kanta domin ta rufa wa kanta asiri da kuma kaucewa kalubalen tattalin arziki, kamar yadda za ku ji yadda rayuwarta ta kasance da irin nasarori da kalubalen da ta fuskanta. Ga yadda hirar tasu ta kasance tare da BILKISU TIJJANI KASSIM.
 Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Sunana Rukayya Usman, amma an fi sani na da Misis Binbaz ina da yara biyu ina zaune a Garin Kaduna ina da takardar babbar difloma (HND) kuma ina dan taba kasuwanci a gida.
 Kina da aure?
Eh tabbas ina da aure
Wanne irin kasuwanci kike yi?
Ina saida kayan kicin da kayan kayata daki da falo, kayan dai kayata gida gaba daya zance.
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
To ni gaskiya kasuwanci yana burgeni, domin tun ina yarinya bana so na ga ana zaman banza duk sai na ji babu dadi mutum ya zauna baya komai.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
To a gaskiya na fuskanci kalubale da yawa a cikin sana’ata, amma bai taba tsorata ni ba saboda duk wani abu da kake so ka cimma buri akansa sai ka sha wahala kafin ka kai ga abin da kake so ka zama shi ya sa ban tsorata ba, na san komai mai wucewa ne gashi kuma ya zama labari.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
Alhamdu lillahi, gaskiya zan ce na gode wa Allah saboda na cimma nasarori da dama gaskiya daga cikin nasarorin da na cimma na bude shago nawa na kaina.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Abin da ya fi faranta min rai a sana’ata shi ne, yadda mutane ke jin dadi wajen saukin kayana kuma suna fada, nima kaina na san ina saukaka kayana ba na cika musu kudi hakan ne ya sa nake samun ciniki sosai kuma ana sayen kayan, gaskiya wannan ba karamin faranta min rai yake yi sosai ba.
Wacce hanya kike bi wajen tallata kayan kasuwarki?
Ina tallata kayan kasuwata ta intanet wato WhatsApp, Facebook, da kuma mutane haka.
Dame kike so mutane su rika tunawa dake?
Ina so mutane su rika tunawa da ni da sauki Home
Ga hidimar gida da yara, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
To a gaskiya babu wani hutu in kin ga na kwanta to dare ne ya yi. Ni da nake nema ina na ga wani hutu babu shi a raina kwata-kwata ma gaskiya.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
A gaskiya babu addu’ar da idan aka yi min nake jin dadin ta kamar a ce min Allah ya kara arziki ya kawo kasuwa Allah ya sa na fi haka
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
mahaifiyata da mahaifina sai mijina gaskiya suna bani goyon baya sosai, sannan kuma suna karfafa min gwiwa gaskiya su ne goyon bayana.
Kawaye fa?
Akwai wadansu daga cikin kawaye na masu tayani gaskiya ina musu godiya ta musamman.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Atamfa da turare saboda ni ma’abuciyar kamshi ce in dai na samu turare to an gama.
A karshe wace irin shawara za ki ba mata?
A daina zaman banza a dinga sana’a