Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa reshen (Arewa-maso-Yamma) Malam Salihu Lukman, ya gargadi jam’iyyar game da zaben tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
A cewarsa, matakin kamar kunar bakin wake ne da kuma tsantsar rashin nazari da ka iya tayar da zaune tsaye a jam’iyyar.
Gargadin na Lukman na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da rahotanni suka bayyana cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin APC na shirin amincewa da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa bayan murabus din Adamu da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp