Dakarun hadin gwiwa na kasa da na sama a karkashin Rundunar ‘Operation Fansan Yanma’ sun zafafa farmakin da suke kai wa fitaccen kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji a jihar Zamfara. Hare-haren baya-bayan nan da sojoji suka kai sun tarwatsa wasu muhimman maboya a Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi, inda Turji da mukarrabansa suka dade suna gudanar da ayyukansu a fili.
Hakan na zuwa ne bayan wasu nasarori da aka samu wanda ya yi sanadiyyar lalata sansanonin ‘yan bindiga da dama a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Zamfara.
Daga cikin sansanonin da aka kai harin sun hada da Zangon Dan Gwandi, Zangon Tsaika, Zangon Kagara, da kuma wata makaranta da Turji ke amfani da ita wajen adana kayan abinci da makamai, inda sojojin suka kona makarantar.
Majiyoyin leken asiri sun tabbatar wa Zagazola Makama cewa, Rundunar mayakan Turji sun samu gagarumar asara. “Mun kashe dansa da wasu da yawa daga cikin mayakansa a yayin farmakin. Na kuma saurari muryar Turji a firgice yana kiran wasu shugabannin ‘yan bindiga guda bakwai su kawo masa dauki amma babu daya daga cikinsu da ya fito, kuma daya daga cikin ‘yan leken asirinsa ya tsira da kyar daga gare mu a yau,” in ji majiyar.
Sahihan bayanai sun nuna cewa, an ga Turji a Zangon Gebe, inda mayakansa dauke da muggan makamai ke kewaye da shi.