Jam’iyyar PRP ta jajantawa iyalan ‘yan Nijeriya da suka mutu a turmutsitsin da ya faru a Ibadan, Abuja, da kuma Jihar Anambra, inda ta ce wannan mummunan lamari ya nuna irin talaucin da jam’iyyar APC mai mulki a karkashin Shugaba Bola Tinubu ta jefa ‘yan Nijeriya a ciki bayan cire tallafin man fetur da kuma aiwatar da wasu manufofin da ba su dace ba wadanda suka yi illa ga ‘yan kasa.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Kwamared Muhammed Ishak, ya fitar wanda aka raba wa ‘yan jarida a Abuja, yayin da ta dora wa gwamnatin tarayya alhakkin wannan lamarin, ta ce ya kamata shugabanni a matakai daban-daban na gwamnati su farka daga dogon barci da suke ciki tare da dauki matakai na gaggawa don magance tushen ire-iren wadannan al’amuran da suke faruwa a kasar nan.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Shinkafar Kirsimeti A Kaduna
- Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti
“Jam’iyyar PRP tana mika jajenta ga iyalai da al’ummomin da suka mutu a wani mummunan turmutsitsin da ya faru a lokacin rabon tallafi a Ibadan ta Jihar Oyo, da Abuja da kuma Anambra. Wadannan munanan abubuwan da suka faru, musamman a Abuja da Anambra, na nuna matukar damuwa da yanayin da ‘yan Nijeriya da suka tsinci kawunansu a cikin a gwamnatin APC.
“Lamarin ya nuna yadda tsananin talauci da fatara da ke wanzuwa a cikin al’ummarmu, al’amuran da ya ta’azzara saboda rashin shugabanci na tsawon shekaru a kasar nan.
“Yayin da muke alhinin rayukan da aka rasa kan wannan lamari, dole ne mu kuma gane cewa wadannan bala’o’i na nuni ne da irin rikicin da al’umma suka tsinci kansu a ciki. Irin wannan lamari yana bukatar daukar matakin gaggawa daga wurin gwamnati a matakai daban-dabn da na al’umma gaba daya. Abubuwan da ke faruwa suna fallasa gazawar ba da fifiko ga walwala da amincin ‘yan kasa a cikin matsanancin yanayin zamantakewa da tattalin arziki.
“Jam’iyyar PRP ta dora wa gwamnatin tarayya da shugabancinta laifi, musamman Shugaban kasa Bola Ahmed Bola, wanda ya ingiza miliyoyin ‘yan Nijeriya ciki bakin talauci, biyo bayan cire tallafin man fetur da aiwatar da wasu manufofin da suka yi tasiri ga marasa karfi a cikinmu. Irin wadannan manufofin sun jefa iyalai da dama cikin matsanancin talauci, wanda ya tilasta musu yin rayuwa cikin matsananciyar wahala a Nijeriya.
“Ya zama wajibi shugabanninmu su farka daga barcin da suke yi, su dauki matakan da suka dace don magance musabbabin wadannan munanan abubuwan da suka faru. Wannan ba wai kawai kira ne na inganta shugabanci ba, amma kira ne na fayyacewa na kare martaba da rayuwar Dan’adam. Lokaci ya yi da shugabanninmu za su saurari kukan jama’a, su kuma ba da fifiko kan matakan da suka dace na siyasa da za su inganta rayukan al’umma maimakon tauye hakkin ‘yan Nijeriya.
“Muna kira ga gwamnati da ta aiwatar da matakan da za su hana wa ‘yan Nijeriya zama mabarata a cikin kasar nan da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa a wajen tarukan jama’a. Sake duba muggan manufofin gwamnatin Tinubu da kawo tsare-tsare masu dorewa da za su rage radadin talauci da samar da ababen more rayuwa ga al’ummarmu shi ne abin da PRP ke bukata.
“Haka nan muna ba da shawara mai karfi da al’ummar kasar nan da su yi watsi da APC da PDP, domin su ne suka haddasa mana bakin talauci da kuncin rayuwa. Shekaru 26 ya isa ya tabbatar da duk wasu alkawarin da jam’iyyun siyasar suka yi wajen kyautata rayuwal al’umma. Dole ne masu zabe su yi abu mai kyau ta yadda kuri’unsu zai sauya akalar abubuwa a kasar nan.
“Tunaninmu da addu’o’inmu sun kasance tare da iyalan da ke cikin bakin ciki a wannan mawuyacin lokaci,” in ji sanarwar.