Rundunar ‘yansandan Jihar Akwa Ibom ta gurfanar da wani mutum mai suna Aniekan James bisa zarginsa da kashe dansa guda daya tilo da Allah ya ba shi, Odudu James, mai shekara 35 a duniya.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Olatoye Durosinmi, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ya gurfanar wanda ake zargin da wasu 268 da aka kama bisa zargin aikata laifuka daban-daban, ana kuma zargin Aniekan da kashe wasu da dama a Legas da Jihar Abia.
- Kyan Wayewar Kai Na Cikin Bambance-Bambancen Dake Akwai Tsakaninsu
- Ziyarar Firaministan Kasar Tsibiran Solomon A Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana Ga Kasar
Kwamishinan ya ce, jami’an hukumar na caji ofis din Ukanafun ne suka cafke wanda ake zargin a ranar 16 ga watan Yunin 2023.
Ya ce, “A ranar 16 ga watan Yunin 2023 ne jami’an caji ofis din Ukanafun suka cafke wani mutum Aniekan James na kauyen Ikot Ndot da ke karamar hukumar Ukanafun bisa laifin harbe dansa mai shekara 35, Odudu James, sakamakon cacar baki da ta shiga tsakaninsu. Ana zargin wanda aka kama din da aikata laifukan kisan mutane da dama a jihohin Legas da Abia.”
Kazalika, kwamishinan ya kuma gurfanar da wani bisa zargin yin garkuwa da mukaddashin shugaban wata jami’a mai zaman kanta da aka sace a lokacin da yake hanyarsa ta komawa gida.
Ya ce, sauran miliyan biyu na kudin fansa da mota kirar Toyota Corolla da aka yi amfani da su wajen aikata laifin an kwato su yayin da shugaban makarantar ya koma cikin iyalansa.
Ya ce an yi garkuwa da mataimakin shugaban jami’ar ne a ranar 14 ga watan Afrilun 2023 a lokacin da ke hanyarsa ta komawa gida. Amma bayan kwana biyu da sace shi, rundunar ra kama wani mai suna Prince Thursday Okon wani tsohon ma’aikacin babban malamin din ne da zargin shi ne ya sace shugaban makarantar.
“An kori Okon daga aiki bisa zargin aikata manyan laifuka. An kama shi ne tare da abokan aikata laifukansu biyu, Sabiour Sunday Luke da Richard Friday, dukkaninsu ‘yan kauyen Ikot Ebam da ke karamar hukumar Mkpan Enin.”
Har-ila-yau, an gurfanar da wani Edu Ime bisa zarginsa da zama mamba na kungiyar asiri.