Babban bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara cire harajin tsaro na intanet kan kowani hada-hadar banki da ‘yan Nijeriya za su yi.
A cewar sanarwar da babban bankin ya fitar, za a fara biyan sabon harajin ne nan da mako biyu masu zuwa.
- Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN Ya Dakatar Da Harajin Tsaron Yanar Gizo
- Almundahana: Kotu Ta Bayar Da Belin Hadi Sirika Da ‘Yarsa
Ga wasu abubuwan da ya dace ku sani kan harajin tsaro na intanet da ‘yan Nijeriya za su dunga biya kamar yadda CBN ya umarta.
Za a rika cire harajin kaso 0.5 cikin dari, kwatankwacin rabin kaso, zai kasance kan dukkanin hada-hadar kudi da aka yi ta yanar gizo ne. Duk kwastoman da ya yi hada-hadar banki ta intanet za a caje shi wannan sabon harajin, kuma bankin da yake ne za su cire kason kai tsaye. Za a sanar da kwastoma ta cikin jadawalin asusun ajiyarsa na cewa an cire wannan kudin.
Haka kuma, bayan bankuna sun cire wannan kudin harajin za su shigar da kudin kai tsaye zuwa asusun harajin tsaron intanet na kasa da ke ofishin babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Za a fara aiwatar da cire kudin ne nan da mako biyu daga ranar da CBN ta sake sanarwa, ranar 6 ga watan Mayu, kuma bankuna za su shigar da kudin zuwa asusun NCF ne a dunkule.
Sannan bankuna za su amfani da tsarin da ke cire harajin da shigar da shi asusun da aka ware. Dukkanin bankin da ya kasa shigar da wannan harajin akwai cin tara da za a yi masa da suka hada da cire kaso biyu cikin dari na kason wannan bankin na shekara-shekara.
Sai dai kum, kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi watsi da wannan umurnin na babban banki kan cire kasha 05 na harajin tsaro ga kowani hada-hadar kudi ta intanet.
Shugaban NLC, Joe Ajaero shi ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja.
Ajaero ya dai yi watsi da sanarwar CBN kan wannan haraji da zai fara aiki nan da wakonni biyu.
A cewar Ajaero, NLC ta yi Allah wadai da wannan mataki tare da kiran gwamnatin tarayya ta gaggauta janye matakin.
Ya ce kakaba wannan harajin zai tagayyara ‘yan kara fiye da halin da ake ciki a yanzu.
Ita kungiyar kokarin tabbatar da adalci ta SERAP ta nuna adawarta da sabon harajin na tsaron intanet.
Kungiyar ta bukaci Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu da ya bai wa Babban Bankin Nijeriya umarnin soke harajin kafin nan da awa 48 kasancewar ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma walwalar al’umma.
Wannan haraji zai zamo doriya ne a kan jerin haraje-haraje da al’ummar Nijeriya ke biya wadanda babban bankin kasar ya kakaba musu.
Cikin su akwai harajin kula da katin ATM, da kula da asusun ajiya, harajin gwamnati, cajin tura kudi daga wani banki zuwa wani da kuma harajin tura kudi ta laturoni.