Hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO), ta sanya karin al’adu 3 na kasar Sin cikin jerin dake wakiltar al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da dan adam ya gada, na hukumar.
Ayyuka 3 na al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba na kasar Sin da suka hada da fasahar saka ta kabilar Li da ta kunshi matse yadi da rini da saka da surfani, da bikin sabuwar shekara na Qiang da kuma fasali da aikin kera gadar katako mai siffar baka ta kasar Sin, sun samu kyawawan sakamakon kariya da ci gaba da inganta kasantuwarsu, tun bayan da aka sanya su cikin jerin al’adun gargajiya dake bukatar kariya ta gaggawa.
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Nemi A Hukunta Jami’n Tsaro Masu Cin Zarifin Mata
- An Fitar Da Rahoton Ci Gaban Duniya Na 2024
Bayan nazari, UNESCO ta yanke shawarar sanya wadannan ayyuka 3 cikin jerinta na al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da dan adam ya gada.
Da wannan karin, yanzu Sin na da siffofin al’adun gargajiya 44 da UNESCO ta amince da su tare da sanya su cikin jerinta na al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da dan adam ya gada. (Fa’iza Mustapha)