Asusun Kula da Kananan Yarana Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadi kan yiwuwar bullar matsalolin ayyukan jin kai a Nijeriya, sakamakon wawakeken gibin kudaden tallafi da ke barazana ga muhimman ayyuka na lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi da kuma samar da ruwa a fadin kasar.
Da yake magana a Maiduguri a ranar Litinin yayin bikin tunawa da Ranar Jin Kai ta Duniya ta 2025, Shugaban Ofishin UNICEF na Maiduguri, Francis Butichi, ya bayyana cewa hukumar ta samu Dala miliyan 95 kacal daga cikin Dala miliyan 255 da ake bukata don gudanar da ayyukan bana, abin da ya bar gibin Dala miliyan 160 (Naira biliyan 240) kashi 67 cikin dari na gibin kudi.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Sanata Wadada Ya Fice Daga Jam’iyyar SDP Bayan Ganawa Da Tinubu
“Muna sane da yankewar kudaden tallafi na duniya da yake barazana ga ayyukan jin kai a fadin duniya. Tasirinsa kuwa yana da matukar muni a matakin cikin gida, inda rikice-rikice, canjin yanayi da barkewar cututtuka ke maimaituwa,” in ji Butichi.
Duk da kalubalen da ake fuskanta, UNICEF ta ce ta kai wa sama da mutum miliyan 1.3 hidimar kiwon lafiya, ta warkar da yara 340,000 da suka kamu da matsanancin karancin abinci mai gina jiki, ta samar da ruwan sha mai tsafta ga mutane 185,000, tare da saka yara 500,000 ‘yan gudun hijira a makarantu.
Butichi ya roki bangaren masu zaman kansu, gwamnati da masu bayar da tallafi da su ci gaba da karin goyon baya ga hukumomin kananan hukumomi da kungiyoyin fararen hula da ke bayar da ayyuka a sahun gaba.
“Bai kamata a dakatar da hidimomin ceto rayuka na abinci mai gina jiki, allurar rigakafi, kiwon lafiya da kariya ga al’ummomin da rikici, ambaliyar ruwa da kuma hijira suka shafa ba,” ya jaddada.
Jihohin Arewa na shirin fuskantar wannan kalubale
A halin yanzu, wasu gwamnatocin jihohin Arewa sun ce suna daukar matakai don rage illolin karancin kudaden da ke tafe.
A Gombe
Daraktan Yada Labarai na Fadar Gwamnati, Ismaila Misilli, ya shaida wa The PUNCH cewa jihar ta riga ta hango kalubalen kuma ta tanadi kasafin kudi don tallafa wa al’umma masu rauni.
“Mun ware kasafin kudi na musamman don kiwon lafiya, ilimi, ci gaban dan’Adam da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta. Don haka, akwai tsari a kan wannan hanya.”
Jihar Kebbi
Ita ma ta bayyana aniyarta na ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen UNICEF.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Alhaji Ahmed Idris, ya ce jihar ta riga ta biya kudin hadin gwiwa kuma ba za ta yi sakaci ba.
Sakkwato
Haka kuma, wani babban jami’i a Sokoto ya tabbatar da cewa Gwamna Ahmed Aliyu kwanan nan ya amince da Naira miliyan 500 a matsayin kudin hadin guiwa don ayyukan UNICEF a fannoni muhimmai, tare da ware karin kudi don aiwatar da ayyuka.
Jigawa
A Jigawa kuwa, jami’an gwamnati sun amince cewa gibin kudi zai iya yin mummunan tasiri ga isar da muhimman ayyukan kiwon lafiya kamar abinci mai gina jiki, rigakafi da kuma samun ruwan sha mai tsabta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp