Wata mata da ’ya’yanta uku sun rasu a ranar Laraba bayan bangon gidansu ya rufta musu sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a unguwar Karauka, Zariya.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Habiba Nuhu, ’ya’yanta mata Hauwa’u da Aina’u, da kuma jikarta Za’uma.
- Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya
- Jimilar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice A Fannin Bayar Da Hidimomi Ta Kasar Sin Ta Kai Yuan Tiriliyan 3.9 A Rabin Farko Na Shekarar Bana
Ɗan uwansu, Malam Ahmed Ibrahim, ya ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 3:30 na dare da 4:00 na safe, inda bangon ya faɗa a kansu.
“Sun rasu nan take bayan sun maƙale ƙarƙashin ƙasa,” in ji shi.
Mai gidan, Malam Nuhu Dogara, ya kuɓuta daga hatsarin.
An kai shi asibiti, inda aka kula da shi sannan aka sallame shi domin halartar jana’izar iyalan nasa.
Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Bello Garba, ya ce ba su samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma sun shirya gudanar da bincike kan lamarin.
An binne mamatan bisa tanadin addinin Musulunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp