Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, ta raba babura 42 da motoci kirar Hilux guda biyu ga jami’an sa ido ga masu fama da cutar tarin fuka a jihar.
Asusun Tallafawa Duniya ne ya bayar da tallafin motocin yaki da cutar AIDS, tarin fuka da zazzabin cizon sauro (GFATM) a matsayin gudunmuwarsu kan yakin da wadannan cututtukan a duk fadin Jihar Kebbi.
- ‘Yancin Kai: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Rage Kudin Man Fetur
- Gwamnatin Kaduna Ta Raba Wa Manoma Taki Buhu 120,000Â
A wajen bikin, Hajiya Zainab ta bayyana muhimmancin kara kaimi wajen yaki da cutar tarin fuka a jihar.
Ta bayyana bukatar karfafa sa ido, musamman a yankunan da ke da wuyar isa, don tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya ba wajen yaki da cutar tarin fuka.
“Wadannan motocin za su inganta zirga-zirgar ma’aikatan kiwon lafiya, da ba su damar isa yankunan da ke nesa, da gano masu cutar tarin fuka a baya, da kuma samar da hanyoyin da suka dace,” in ji ta.
“Dole ne mu ci gaba da wayar da kan jama’a game da alamun cutar tarin fuka da magani, rage kyama, da tabbatar da samun damar yin gwaji da ba da magani a kyauta.”
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta wallafa rahoton cewa cutar tarin fuka ta kasance babbar damuwa ga lafiyar jama’a.
Ta ce akalla mutane miliyan 2.5 ne suka kamu da cutar tarin fuka a yankin Afirka a 2022.
Shirin na WHO ya kawo karshen cutar tarin fuka yana da nufin rage tarin fuka da kashi 90% sannan sabbin masu kamuwa da cutar da kashi 80 cikin dari nan da shekarar 2030.
Dokta Moses Onoh, jami’in fasaha kan cutar tarin fuka a WHO, ya yaba wa kokarin Hajiya Zainab, ya kuma shawarci jami’an da su yi amfani da motocin yadda ya kamata.
Kwamishinan lafiya na jihar, Comrade Yunusa Musa Isma’il ya yabawa masu hannu da shuni da kuma uwargidan Gwamnan Jihar bisa wannan tallafi da suka bayar.
Wannan shiri ya nuna jajircewar Jihar Kebbi wajen yaki da cutar tarin fuka da kuma tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya ga ‘yan jihar.