Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa nakasassu 250 tallafi a Zamfara karkashin Shirin RHI na rabawa mata tallafi Jari.
Shirin an yi shi ne don bai wa tsoffin sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro wadanda ke fuskantar kalubale wajen bunkasa ƙananan kasuwancinsu.
- Sheikh Zakzaky Ya Halarci Addu’ar Bakwai Ta Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Hukuma Ta Gargaɗi Jama’a Kan Amfani Da Wuta A Lokacin Hunturu A Kano
Yayin bada tallafin, Sanata Oluremi Tinubu wadda ta samu wakilcin uwargidan gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda, ta bayyana farin cikinta da kaddamar da Shirin tallafin Tattalin Arziki ga Nakasassu, a karkashin Shirin bada Jari ga Jama’a na RHI.
Oluremi Tinubu, ta ce taron yana da matukar muhimmanci domin ya zo daidai da ranar Nakasassu ta Duniya kuma ana kaddamar da shi a lokaci guda a fadin jihohi 36, da babban Birnin tarayyar kasar nan da kuma Kungiyar Matan Jami’an Tsaro da ‘Yansanda (DEPOWA).
Ta ce, kasa na kara karfi lokacin da aka bai wa kowane mutum ikon bayar da gudummawa mai ma’ana.














