Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu; ta tallafa wa tsofaffi da dama da Naira 250 kowannensu a Jihar Kogi, a kashi na biyu na shirin tallafa wa tsofaffi da aka fi sani da (Renewed Hope Initiative Elderly Support Scheme).
Jaridar Blueprint ta rawaito cewa, masu cin gajiyar tallafin ‘yan shekara 65 zuwa sama; daga cikin kananan hukumomi 21na Jihar ta Kogi.
- Bangarorin Da Suka Fi Samun Kaso Mai Tsoka A Kasafin Kudin 2025
- Yahaya Bello Ya Samu Beli Bayan Cika Sharudan Kotu
A wata sanarwa da ofishin yada labarai na Uwargidan Gwamnan Jihar Kogi ta fitar a ranar Talatar da ta gabata ta ce, “A wajen mika kyaututtukan kudi ga wadanda suka ci gajiyar kudin a gidan gwamnati da ke Lokoja, Sanata Oluremi Tinubu; ta wakilci Uwargidan Gwamnan Jihar Kogi, Hajiya Sefinat Usman Ododo; ya kara da cewa, kimanin Naira biliyan biyu za a raba wa wadannan tsofaffi a dukkanin fadin jihohi 36; ciki har da babban birnin tarayya, Abuja.
“Shugabannin RHI na jihohi 36 ciki har da Abuja da kuma kungiyoyin mata na sojoji da ‘yansanda (DEPOWA), sun karbi Naira miliyan 50 kowannensu, inda kowane mutum guda zai samu kimanin Naira 200,000.
Bugu da kari, za a aiwatar da gwajin lafiya kyauta tare da bayar da wasu kayayyaki su ma kyauta.” Uwargidan Shugban Kasar ta bayyana haka, in ji jihar.
A cewar ofishin yada, “Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa, za a bai wa kowane mutum guda Naira 200,000; a matsayinsu na wadanda suka yi ritaya kuma tsufa ya cin musu.
Ya ci gaba da cewa, “Uwargidan Shugaban Kasar ta bayyana za a yi gwajin lafiya tare da bayar da wasu kayayyaki kyauta ga wadanda ake sa ran za su ci gajiyar shirin a dukkanin fadin wannan kasa.
“Yayin da take taya wadanda suka ci gajiyar shirin murnar zabarsu, Uwargidan Shugaban Kasar ta bukaci manyan masu kula da shirin da su ba da fifiko wajen kula da lafiyarsu akai-akai.”