Dan wasan gaban Real Madrid, Vinicius Jr ya tsawaita kwantiraginsa a Real Madrid har zuwa shekarar 2027.
Dan wasan na Brazil, mai shekara 23, ya ci kwallo 63 a wasanni 235, ya kuma lashe kofi tara a Real Madrid ciki har da gasar zakarun turai a 2022.
- Kasar Sin Ta Gudanar Da Taron Koli Kan Harkokin Kudi
- Shugaba Xi Jinping Ya Amsa Wasikar Mashahurin Masanin Kimiyya Da Fasaha Na Kasar Cuba
Vinicius, wanda kwantiraginsa zai kare a shekara mai zuwa, ya koma Real Madrid kan fam miliyan 38 tun yana dan shekara 18 daga kungiyar Flamengo a shekarar 2018.
“Na yi matukar farin ciki da sabunta kwantiragina domin wannan mafarki ne a gare ni,” in ji shi a wani faifan bidiyo da ya yi.
“Ina fatan zan ci gaba a nan tsawon shekaru da yawa kuma ina so na ci gaba da zura kwallaye da yawa kuma na lashe kofuna da yawa.”
A ranar Litinin ne Vinicius ya kasance na shida a zaben Ballon d’Or na maza, wanda dan wasan gaban Argentina Lionel Messi ya lashe kuma aka ba shi lambar yabo ta Socrates saboda aikin da ya yi a fannin harkar ilimi da yaki da wariyar launin fata a Brazil.