• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wa Ya Dace Al’umma Su Zaba?

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
in Bakon Marubuci
0
Wa Ya Dace Al’umma Su Zaba?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Daga lokacin da aka kada gangar siyasa ta zaben 2023, ‘yan siyasa daga kowace jam’iyya da take da rajista a Nijeriya suka fara baza dabarunsu ta neman kuri’un jama’a domin samun damar darewa madafun iko.

A ‘yan shekarun baya, manyan dabarun da ‘yan siyasar suka fi amfani da su su ne: sayo shinkafa, gishiri, sukari, sabulu, da atamfofi domin rabawa ga jama’a don a zabensu.

  • Hanyoyin Kula Da Fatar Jiki (4)
  • Zamanintarwa Irin Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Shimfida Zaman lafiya Da Kwanciyar Hankalin Duniya

Kan wadannan ‘yan kayayyaki da ba su fi su yi wa mutum mako guda a gidansa ba (kason da aka ba shi) sai a jefa kuri’a ga wanda idan ya ci, ya cika wandonsa da iska ke nan sai kuma wani lokacin zaben bayan wa’adin shekara hudu.

Amma ga dukkan alamu a wannan kakar siyasar, dabarun ‘yan siyasar na daukar sabon salo, daga sayen kayan masarufi zuwa bayar da zunzurutun kudi da kuma amfani da yanayin da mutane suka tsinci kansu a ciki wajen kai musu tallafin gaggawa.

A kwanan nan baya ga matsalar tsaro, babu wani abu da ke ci wa jama’a tuwo a kwarya kamar ambaliyar ruwa.

Labarai Masu Nasaba

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

Waraka Daga Bashin Ketare

Yanzu haka ‘yan siyasa sun yi nisa wajen nuna tausayawa da alhini da kuma bayar da gudunmawa ga jama’ar da ibtila’in ya shafa.

Dama dai tun a farkon daminar bana, hukumar kula da harkokin albarkatun ruwa ta Nijeriya (NIHSA) tare da takwararta ta hasashen yanayi ta NIMET sun yi hasashe cewa za a samu yiwuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 23 da ke jihohi 32 har da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Hakan ya kuma faru, wanda ‘yan siyasa suke ta amfani da wadanda ibtila’in ya fada musu wajen tallafa manufofinsu ta siyasa.

‘Yan takara musamman masu neman shugabancin kasa sai kai ziyara inda wannan lamarin ya auku suke tare da bayar da tallafi ga wadanda annobar ta shafa.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu ya ba da tallafin Naira miliyan 50 ga jama’ar da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Jigawa, ga na baya-bayan nan da ya bayar da Naira milyan100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.

Shi kuwa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya ziyarci Jihar Benuwe, inda ya bayar da tallafin Naira miliyan biyar.

Haka kuma ya kai ziyara a Jihar Bayelsa inda ya jajanta masu da nuna jimaminsa kan faruwar lamarin.

Atiku Abubakar da ke neman takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP shi maya bai wa wadanda ambaliyar ruwa na kasuwar Kantin Kwari da ke Kano tallafin Naira milyan 50.

Na baya-bayan nan kuwa shi ne wanda ya bai wa wadanda ibtila’in ya shafa a Jihar Yobe kayayyakin abinci da sauran wasu abubuwa.

Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso yayi nasa kokarin duk da babu wata shaida baro-baroa fili.

Haka abubuwan suke ga kananan ‘yan siyasa masu neman takara a matakin jihohi da tarayya wajen jajanta wa al’ummar da ibtila’in ruwa ta shafa tare da ba su tallafi, wanda ko ba a fada ba, mai hankali ya san don yakin neman zabe suke yi.

Yanzu muna so al’ummar Nijeriya ta yi wa kanta adalci tare da auna wadannan ‘yan takarar guda biyu da za mu kawo a kasa.

Wai da dan takarar da ya ziyarci wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa, ya tashi takanas-ta-kano ya tafi inda suke ya jajanta musu, har ma saboda tausayi ya zubar da hawaye amma bai ba su kobo ba.

Da kuma dan takarar da shi bai samu ziyartar inda suke ba, amma sai ya aike musu da da makudan kudade da sakon jaje.

Shin wa ya kamata su zaba? Ina fatan wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su wadanda suka hada da Hausawa da Yarbawa da Inyamurai za su bayar da sakamako iri daya.

Domin, cikin wadannan ‘yan takarar biyu, wanda ya nuna alhini har da sa abin a cikin ransa tare da zubar da hawaye, ana ganin kilazai fi tausaya musu idan ya samu madafun iko, watakila ma ya magance musu abin da ke haddasa ambaliyar har Abadan.

Yayin da wanda ya ba su kudi kuma bai shigar da abin cikin ransa, na iya biris da su saboda ya sallame su tun kafin ya hau mulki.

Siyasar kudi ta riga ta ratsa zukatan ‘Yan Nijeriya da dama wanda shawo kan wannan lamari na da matukar wahalar gaske.

Idan za a iya tunawa, a Shirinmu na Manhajar Podcast na Barka Da Hantsi Nijeriya da muka gabatar a farkon watan Oktoba tare da daya daga cikin dattawan kasa, Dakta Hakeem- Baba Ahmad, ya bayyana hatsarin sayen kuri’u da kuma yadda za a iya samun sahihin zabe a 2023.

Haka ma masu shirhin al’amurar siyasa suna ta kira ga ‘yan Nijeriya da su yi kokarin kauce wa sayar da kuri’unsu ga dukkan wani dan takara, su yi kokarin zaben ‘yan takarar da suka dace.

Wannan ne ya sa kungiyoyin arewa daban-daban suka taru a karkashin inuwa guda suka tattauna da ‘yan takarar domin jin manufofinsu da yadda za a kauce wa fadawa gidan jiya a yankin arewa.

Wani babban abin takaici dai shi ne, yadda ‘yan siyasa ke jan ra’ayoyin mutane da ‘yan kudi kalilan.

Inda a baya suke bayar da kudi daga Naira 10,000 zuwa 5,000, amma a halin yanzu kudin bai wuce dubu daya zuwa biyu, kai akwai ma idan ake bai wa mutum dari biyar ya sayar da ‘yancinsa na tsawon shekaru hudu masu zuwa, kamar yadda aka ga misalign haka a zabukan da aka yi a wasu jihohin kudu a kwanan bayan nan kamar Ekiti da Osun.

Wannan babban abin takaici ne ga al’ummar Nijeriya, musamman a daidai lokacin da abubuwa suka rikice. Ana tunanin babu abinda zai iya sauya matsalolin da suke addabar Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya face shugabanci nagari.

Idan kuwa haka ne, to ya kamata ‘yan Nijeriya su yi karatun ta-natsu wajen sanin dan takarar da za su zaba da zai kawo kyakkyawan shugabanci ba tare da la’akari da kabilanci, addini ko kuma bangarenci.

Yana da matukar muhimmanci ‘yan Nijeriya su guji kwadayin kudaden da ‘yan takara suke ba su wajen zaben shugaba ko wakili da zai jagoranci al’umma na tsawon shekaru hudu.

Sayen kuri’u wajen zaben shugaba ba zai taba haifar wa da al’ummar Nijeriya da mai ido ba,zai ci gaba da jefa kasar da mutanen kasar a cikin mawuyacin hali, baya ga wanda suke fuskanta yanzu haka!


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yan TakaraHakeem Baba AhmedKuri'a Masu ZabeSiyasaZaben 2023
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ruhin Hanyar Ruwa Ta Red Flag Zai Ci Gaba Da Kasancewa Har Abada

Next Post

Wang Yi Ya Gana Da Jakadan Amurka Dake Kasar Sin

Related

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
Bakon Marubuci

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

4 weeks ago
Waraka Daga Bashin Ketare
Bakon Marubuci

Waraka Daga Bashin Ketare

1 month ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20]

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19]

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]

2 months ago
Next Post
Wang Yi Ya Gana Da Jakadan Amurka Dake Kasar Sin

Wang Yi Ya Gana Da Jakadan Amurka Dake Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.