Kawo yanzu dai za a iya cewa ‘yan wasa da dama ne suke neman lashe gasar kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon’d’Or wadda jaridar kasar Faransa take bayarwa duk shekara.
A ranar 4 ga Satumba za a sanar da jerin wadanda za su yi takarar zama gwarzon ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, inda za a yi la’akari da kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 tare da kuma manyan gasa da aka gudanar a bazara.
- Ko Mbappe Zai Lashe Kofin Zakarun Turai Da Ballon d’Or A Real Madrid?
- Sassa Daban Daban Na Mutunta “Ka’idar Sin Daya Tak a Duniya” Da Adawa Da Ballewar Yankin Taiwan
Zakakuran ‘yan wasa guda biyu, Binicius Jr da Jude Bellingham na Real Madrid sun kasa lashe gasar cin kofin nahiya da suka buga da Brazil da Ingila, hakan na nufin kambun ya zama na mai rabo ka dauka.
Sai dai duk da haka akwai zakakuran ‘yan wasa guda shida da ake sa ran dayan su zai iya yin nasara a bikin da za a yi a ranar 28 ga watan Oktoba a birnin Paris na kasar Faransa:
Jude Bellingham (Real Madrid da Ingila)
AGES
Matashin dan wasan tsakiya na Ingila Bellingham, mai shekara 21, ya taka rawar gani a kakar wasansa ta farko a Real Madrid bayan ya bar kungiyar Borussia Dortmund a bara.
Dan wasan ya ci kwallaye 23, ciki har da guda biyu da jefa wa Barcelona a gida da waje a gasar La Liga – ya kuma zura 13 yayin da suka lashe babbar gasar Sifaniya da gasar Zakarun Turai a kakar wasan da ta gabata ta 2023 zuwa 2024.
Ya kuma nuna bajintarsa a gasar Euro 2024 inda ya farke kwallon da aka ci Ingila a karin lokaci a wasan zagayen ‘yan 16 da suka buga da kasar Slobakia sai dai da ya yi zaburar da Ingila ta yi nasara a kan Sifaniya a wasan karshen gasar, mai yiwuwa ya zama dan wasan Ingila da zai lashe kyautar Ballon d’Or na farko tun bayan Michael Owen a shakarar 2001.
Rawar da ya taka a bana:
Wasanni: 54.
Kwallaye da ya ci: 27.
Wanda ya taimaka: 16.
Kofuna da ya lashe: La Liga, Kofin Zakarun Turai, Spanish Super Cup.
Lamine Yamal (Barcelona da Sifaniya)
AGES
Matashin dan wasan gefe na Barcelona Yamal ya riga ya yi kakar wasa mai ban sha’awa musamman ganin cewa shekarunsa 16, yayin da ya buga wasanni 50 a kungiyar.
Hakan ya sanya shi zama dan wasa mai mafi karancin shekaru da ya buga wasanni 50 a Barcelona sannan kwallaye guda hudu da ya taimaka aka zura a gasar Euro 2024 a Jamus sun yi daidai da adadi mafi yawa a gasar cin kofin nahiyar Turai – kuma ya zura kwallo mai ban sha’awa a wasan da suka doke Faransa a matakin kusa da na karshe.
Yamal ya kasance dan wasa mai mafi karancin shekaru, wanda ya zura kwallo a raga kuma ya yi nasarar lashe gasar cin kofin Nahiyar Turai, ya cika shekara 17 kwana daya kafin wasan karshen gasar, shi ne aka nada gwarzon matashin dan wasa a gasar.
Shahararren dan wasan Brazil Ronaldo, mai shekara 21, shi ne matashin dan wasa mafi karancin shekaru da ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 1997 a lokacin yana kungiyar Inter Milan.
Bajintarsa a wannan kakar:
Wasanni: 64.
Kwallaye da ya ci: 10.
Wanda ya taimaka: 14.
Kofuna da ya lashe: Euro 2024.
Binicius Jr (Real Madrid da Brazil)
Daman dai an dade ana alakanta dan wasan gaban na Real Madrid Binicius, mai shekara 24, da lashe kyautar Ballon d’Or bayan ya buga wa kungiyarsa ta lashe gasar La Liga da kuma gasar Zakarun Turai.
Dan wasan ya kasance wamda ya fi zura wa Real Madrid kwallo a raga a kakar wasan da aka kammala inda ya zura kwallaye 24, sannan ya taimaka aka zura wasu kwallayen guda 11.
Samun nasarar lashe gasar Copa America da Brazil ce za ta kusan tabbatar da nasararsa na lashe kyautar, amma Uruguay ta yi waje da su a bugun fanariti, a wasan da Binicius bai buga ba saboda dakatarwar da aka yi masa bayan karbar katin gargadi biyu a matakin rukuni.
Dan Brazil na karshe da ya lashe kyautar Ballon d’Or shi ne Kaka a shekara ta 2007, tun lokacin Neymar ne kawai ya ji kamshin ta da ya kare cikin ukun farko. Rawar da Binicius ya taka a kakar da ta wuce:
Wasanni: 49.
Kwallaye da ya ci: 26.
Wanda ya taimaka: 11.
Kofuna da ya lashe: La Liga, Champions League, Spanish Super Cup.
Lionel Messi (Inter Miami da Argentina)
AGES
Idan aka ce Messi a maganar lashe wannan kyauta an gama magana domin Messi, mai shekara 37, shi ne dan wasan da ya fi samun nasara a tarihin Ballon d’Or, inda ya lashe sau takwas, ciki har da shekarar da ta gabata, sakamakon yadda ya jagoranci Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya.
Har yanzu Messi yana cikin wadanda ake tunanin zai iya lashe kyautar amma zai zama abin mamaki idan ya yi nasara kuma ya zura kwallo daya kacal a gasar cin kofin Copa America da Argentina ta yi lashe a bana, a karawar da suka yi da Canada a wasan dab da na kusa da na karshe, ya ji rauni a wasan karshe, inda da yawa ke ganin bai tabuka abin a zo a gani ba, amma kuma Messi bai ci kofi ko daya da Inter Miami ba a kakar wasan da ta gabata.
Rawar da ya taka a bana:
Wasanni: 39.
Kwallaye da ya ci: 28.
Wanda ya taimaka: 17.
Kofuna da ya lashe: Copa America 2024.
Rodri (Manchester City da Sifaniya)
Shahararren dan wasan tsakiyar kasar Spaniya, Rodri, mai shekara 28, ya yi rashin nasara a wasa daya ne kacal a duk kakar wasan da ta gabata a Manchester City da kuma kasarsa (ban da bugun fanareti) – wasan karshe na cin kofin FA da Manchester United.
Ya yi nasarar lashe kofuna uku a kakar wasan da Manchester City, sa’annan ya kara da Euro 2024 a bazara da Sifaniya amma ya ji rauni ne a lokacin hutun rabin lokaci a wasan karshe na gasar cin kofin Turai da Ingila, amma ya riga ya yi abin da ya dace don an bashi kyautar dan wasan da ya fi fice a gasar.
Sai dai kuma a tarihi babu wani dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ya taba lashe kyautar Ballon d’Or a lokacin da yake buga wa kungiyar wasa sai watakila a kansa.
Rawar da ya taka a bana:
Wasanni: 63.
Kwallaye da ya ci: 12.
Wanda ya taimaka: 14.
Kofuna da ya lashe: Premier League, Uefa Super Cup, Club World Cup, Euro 2024.
Dani Carbajal (Real Madrid da Sifaniya)
ADRID FC
A tarihi ba a taba tsammanin dan wasan baya na gefen dama Carbajal, mai shekara 32, zai iya fitowa cikin ‘yan takarar Ballon d’Or ba, amma ya zama daya daga cikin mutane 12 da suka buga kuma suka lashe wasan karshe a gasar Zakarun Turai da na Nahiyar Turai (EURO) a kakar wasa guda.
Tsohon dan wasan ya zura kwallon farko da Real Madrid ta ci a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai da suka doke Borussia Dortmund, sannan kuma ya ci wa Sifaniya kwallo a gasar Euro 2024 da ta doke Croatia a matakin rukuni.
Idan har ya yi nasara Carbajal zai zama dan wasan baya na gefen dama na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or a duniya duk da cewa dan wasa Fabio Cannabaro, dan wasan tsakiya na baya, ya taba lashe wa.
Rawar da ya taka a bana:
Wasanni: 54.
Kwallaye da ya ci: 7.
Wanda ya taimaka: 8.
Kofuna da ya lashe: La Liga, Champions League, Spanish Super Cup, Euro 2024.