Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya bukaci Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kara wa al’ummar jihar Yobe wa’adi na daban, da zai bayar da damar canza tsoffin takardun kudadensu, sabanin 31 ga watan Janairun da ya saka da farko.
Gwamnan ya bayyana hakan a sanarwar manema labaru, ranar Lahadi, mai dauke da sa-hannun Daraka Janar kan hulda da yan jaridu da Kafafen yada labaru, Mamman Mohammed, inda ya ce Gwamna Buni ya bayyana cewa neman ƙarin wa’adin ya zama dole sakamakon yadda jihar ke fama da karancin bankuna.
Gwamna Buni ya kara da cewa, kananan hukumomi hudu ne kacal cikin 17, a fadin jihar suke da bankuna, al’amarin da ya ce zai yi wahala mutane su samu damar canja kudaden su a kwanaki 13 da suka rage a wa’adin da Babban Bankin Nijeriya ya gindaya.
“Sannan kuma wasu daga cikin bankunan da suke da rassa a wasu kananan hukumomin, dole ya sa sun rufe sakamakon rikicin Boko Haram da ya yi kamari, kuma har yanzu basu sake bude su ba a fadin jihar.”
“Saboda haka muna kyautata zaton CBN zai kula wajen bai wa irin wadannan wurare kulawa ta musamman sakamakon bukatu na musamman, domin kaucewa jawo asarar kudaden jama’a.”
“Kuma muna kira ga CBN da sauran bankunan Kasuwanci su kalli wannan bukata ta jama’a cikin gaggawa wajen nemawa al’umma mafita tare da dakile halin fargaban da ake ciki.”
“A matsayinsa na mai sanya ido, yana da kyau Babban Bankin Nijeriya ya tabbatar cewa bankunan Kasuwanci sun bude rassan su a shalkwatar kananan hukumomin saboda a halin yanzu zaman lafiya ya samu a fadin jihar Yobe.” In ji Gwamna.
Bugu da kari, Gwamna Buni ya kara da cewa, ci gaban da ake samu ta fannin tsaro a jihar Yobe da Arewa Maso Gabas baki daya, babu wata fargabar da za ta hana bankuna su sake bude rassan su a shalkwatar kananan hukumomin da manyan garuruwa.
Har ila yau, Gwamna Buni ya sake nanata cewa, akwai fargaba matikar ba a dauki matakin gaggawa ba, saboda ko shakka babu jama’a da dama za su fuskanci barazanar karayar tattalin arziki, da dalilin canjin kudin.
“Sannan a matsayinmu na gwamnati, wajibi ne mu yi dogon nazari don kaucewa kalubalen da zai jawo, wanda lalle akwai bukatar CBN, Babban Bankin Nijeriya ya dubi lamarin nan tare da daukar matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar.” In ji Gwamna Buni.