Shafin taskira, shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin halin da muka tsinci kammu a ciki dalilin haka yasa wannan shafin zai ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu.
- Ambaliya: Uwargidan Gwamnan Yobe Ta Janjanta Wa Al’ummar MaiduguriÂ
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin A Matsayin Hutun Maulidi
Sunana Bilkisu Maharazu Daga Katsina ina zaune a Abuja.
Hanyoyin daya kamata abi a magance ko ince akawo karshen matsalar man fetur a Nageriya shine ta hanyar maido da tallafin man fetur da aka cire shine kadai hanyar da za,a magance wannan matsalar, karin albashi zuwa minimum wage duk bashi bane sannan abama pribate company dama su bude nasu mutane kamarsu dangote da sauransu wadanda keda kishin kasa don cigaban al,umma baki daya ba wadanda ke wowarin haddasa matsaloli tsakanin al, umma ba, wannan itace hanyar da tadace abi don kawo karshen wannan matsala ta man fetur.
Assalamu alaikum warahmatullahi wabara katuhu!
Sunana Rabi’atu Abdullahi Muhammad daga Jihar Kano
Hanyoyin da ya kamata abi don kawo karshen wannan hali da al’ummar Nageriya suke ciki shine ta inda akaho tanan za’a sauka wato ina nufin amaido da tallafin mai da’aka cire sannan kuma aja kunnan ‘yan kasuwa da idan kaya ya sauka suma suyi hakori su saukeshi in ba haka ba asaka musu takunkumi duk wanda bai sauke ba za’a kamashi. Ina ganin idan anbi wannan hanyar da yarda Allah za’a samu sauki Allah yasa mudace.
Assalamu alaikum!
Sunana Abdurrahman Tijjani daga Jihar Jigawa ina zaune a Abuja
Hayoyin da za’a bi wajen magance wannan matsala da muke ciki mudage da addu’a dayi istigifari mu koma ga Allah in sha Allah za’asamu sauki Allah maji rokon bawansane, sannan kuma shi shugaba asamu masu bashi shawara akan yasan halin da al’umarsa suke ciki idan da hali kuma zaiyiyu a maida tallafin mai da aka cire saboda munan ba kasar waje bace su kasar waje suna kokari suga cigaban al’umma sannan basu da san zuciya da kowa da kowa duk daya ne sannan albashinsu ba irin namu bane sunada albashi mai tsuka yadda kowa albashinsa ya isheshi ya rikeshi mu kuma fa a halin da ake ciki yanzu ba ko’ina ne akecin abinci sau uku a rana ba, kai bama maganar sau uku a ranaba abincin ma babu ko sau daya a wani wajen. Allah yasa mudace.
Sunana Usman Sani daga Abuja
Don kawo karshen yawan karin farashin mai, gwamnati na iya daukar wasu matakai. Wadannan sun hada da kayyade farashin mai ta hanyar tallafi, wallafa amfani da hanyoyin makamashi masu madadin kamar hasken rana ko motocin lantarki, inganta wallafa matatun mai don rage dogaro da man da ake shigo da shi daga kasashen waje, da kuma magance matsalolin da suka shafi wadatar mai da buwata a kasuwar mai.
Suna na Fatima Muhammad daga Hadejia
Don kawo karshen yawan karin kudin mai abin da yakama gwamnati tayi shine ta dawo mana da tallafin mai da tacire saboda tunda ta cire rayuwa ta kara tsananta a Nigeria mutane suna cikin wahala rashin abinci rashin tsaro tsadar rayuwa wasu sun rasa muhallinsu sun rasa garuruwansu bama ta abinci suke ba sude gasunan yanda suke ba kawai de suna suna raye Allah yasa mudace.
Sunana Ibrahim Musa daga Jihar Kaduna
Akwai Hanyoyi da dama da Gwamnati zasu iya bi dan kawo karshen yawan karin farashin Mai kaman:
1. Dawo da Tallafi (Subsidy)
2. Gwamnati ta gina ko ta gyara matatan hako Mai Wato Refineries kenan
3. Gwamnati su kara wa Dangote goyan baya
4. Gwamnati su kara wa ‘yan kasuwa goyan baya ga wanda suke cikin harka na mai da tallafi domin a samu wanda zasu gina matatan mai.
Sunana Alkazim Garba daga Jihar Filato
Gabatarwa:
Karancin man fetur da tsadar man fetur sun dade suna zama babban kalubale ga ‘yan Najeriya, wanda ke shafar rayuwarsu ta yau da kullum da kuma harkokin tattalin arziki. Batutuwan sun taso ne daga abubuwa daban-daban kamar rashin isassun karfin tacewa, kalubalen ababen more rayuwa, fasa-kwauri, da hauhawar kasuwanin duniya. Wannan labarin ya ba da shawarar mafita mai amfani da nufin magance wadannan matsalolin da rage farashin mai ga ‘yan Najeriya.
Inganta matatun mai a kasar:
Matakin farko na magance karancin man fetur yana kara karfin tacewa cikin gida. Ya kamata hukumar kula da Man Fetur ta Najeriya (NNPC) ta ba da fifiko wajen gyara matatun mai da gina sabbi. Hakan ba zai rage dogaro da man da ake shigowa da shi daga waje ba har ma ya daidaita farashin saboda karuwar kasa tsakanin masu kera.
Zuba Jari a makamashi Mai Sabunta:
Najeriya tana da albarkatu masu yawa na hasken rana, iska, ruwa, da albarkatun halittu. Zuba hannun jari a hanyoyin samar da makamashi na iya taimakawa wajen karkatar da makamashin kasar da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Tsarin gida na hasken rana, kananan grid, da manyan masana’antar wutar lantarki sune yuwuwar yunkurin da za a iya bincika.
Inganta kayan aikin sufuri:
Inganta kayan aikin sufuri yana da mahimmanci don ingantaccen rarraba mai da rage asara yayin tafiya. Habaka bututun mai, gina karin wuraren ajiya, da saka hannun jari a manyan motocin dakon man fetur na zamani zai rage digogi da kuma hana dogaro da kai ga tashoshin lodin manyan motocin da ke fuskantar layukan da za a yi amfani da su.
Aiwatar da Matsanancin Matakan hana fasa kwauri
Kayayyakin man fetur da ake fasakwaurin suna taimakawa sosai wajen karanci mai da rashin daidaiton farashi a Najeriya. Karfafa tsaron kan iyaka, habaka fasahar sa ido, da kuma sanya hukunci mai tsauri a kan masu laifi zai hana ayyukan da ba bisa ka’ida ba da kuma ci gaba da yin gasa ta gaskiya a cikin masana’antar.
Habaka sufurin Jama’a
Karfafa amfani da zirga-zirgar jama’a yana rage adadin motocin da ke kan hanya, ta yadda zai rage yawan bukatun mai. Tallafin gwamnati da ingantattun ayyukan basa iya sa wannan zabi ya zama abin sha’awa ga masu ababen hawa da ba da gudummawa ga ci gaban zirga-zirgar ababen hawa.
Kammalawa:
Magance karancin man fetur da rage kashe kudade na bukatar tsarin da ya shafi bangarori da dama da suka hada da saka hannun jari a matatun mai, sabunta makamashi, inganta ababen more rayuwa, hada-hadar manufofin, matakan hana fasa kwauri, inganta sufurin jama’a, da inganta tsarin tsari. Ta hanyar aiwatar da wadannan dabarun, Najeriya za ta iya samun dorewa na dogon lokaci, samun araha, da kuma samun dama a fannin man fetur dinta, wanda a karshe zai amfana duka kasuwanci da gidaje.