Tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da kasancewa kan yanayi mai karko, inda cikin watan da ya gabata, kokarinsa na ingiza ci gaba mai inganci ya habaka.
Cikin watan Augusta, sayayyan kayayyaki ya karu da kaso 2.1. Yayin da darajar kayayyakin da masana’antu ke samarwa a kasar, wadda ke da muhimmanci ga alkaluman tattalin arziki, ya karu da kaso 4.5 a watan na Augusta. Jarin da Sin ta zuba kan kadarori kuma, ya karu da kaso 3.4 cikin watanni 8 na farkon bana, inda jimilarta ta kai yuan triliyan 32.94, kwatankwaci dala triliyan 4.64. (Fa’iza Mustapha)
Talla