• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wace Irin Asara Girgizar Kasa Ta Haifar A Maroko?

by Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
Maroko

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Ziyarar masu yawon bude ido zuwa tsaunukan Maghreb a baya ta kasance wata kafar samun kudaden shiga da ayyukan yi a yankin da ke fama da fatara.

Makonnin baya, kafin aukuwar ibtila’in girgizar kasar da ta girgiza Morocco, Abdessamad Elgzouli ya kan jagoranci mutane masu zuwa kasar yawon bude ido, inda yake jagorantar su zuwa tsaunukan kasar dake yankin al’ummomin Maghreb kuma matsugunin kabilar Berber ko kuma Amazigh.

  • A Shirye Sin Take Ta Inganta Hadin Gwiwa Da UNESCO Domin Samar Da Ci Gaba Da Zaman Lafiya A Duniya
  • Manyan Batutuwa 7 Da Za Su Turnike Zauren Majalisa Bayan Dawowa Hutu

Yanzu sabuwar sana’ar Elgzouli ita ce taimakawa wajen kafa rumfuna a sansanoni a Amizmiz, inda daruruwan mutanen da suka rasa muhallansu a sakamakon girgizar kasar da ta auku cikin wannan watan su ke.

Elgzouli wanda yake kewaye cikin gidan shi wanda ya lalace duk da cewa bai rushe ba, ya ce, abin da ya wuce ya zama tarihi”.

Girgizar kasar mai karfin 6.8 a ma’auni ta kashe akalla mutum 3,000, ta kuma shafe gidaje a kauyukan da ke tsaunukan, kana ta lalata makarantu, asibitoci da gidaje a gundumomi 5 da lamarin ya fi shafa. Cikin ‘yan dakikai ta shafe tushen tattalin arzikin kasar na yawon bude ido wanda al’ummomin na Moropcco masu fama da talauci da karancin ci gaba suke alfahari da shi wajen samun kudaden shiga.

Yanzu yankin yana fuskantar matsalar sake farfado da gine-ginen da suka rushe a daidai sa’adda ake tunkarar yanayi mai tsanani na hunturu wanda zai sa aikin farfadowar ya yi matukar wuya sannan kuma ya dada ta’azzara matsin rayuwa ga dubban ‘yan Marocco da ke rayuwa a cikin rumfunan da aka kafa a can tudun tsaunnukan.

Yayin da gwamnatin kasar ta yi alkawarin zuba tsabar kudi dala biliyan $11.7 da zummar taimaka wa mutanen da girgizar kasar ta shafa su miliyan 4 sake farfado da rayuwarsu, kwararru sun ce matsalar kai dauki ta habaka fiye da haka yadda ake tsammani. Tun farkon watan nan dai, wani binciken Amurka kan yanayi ya kiyasta ibtila’in cewa zai dada tsananta tabarbarewar arzikin kasa, kana ta yiwu ta lakume wa kasar kaso 8 daga kudaden shigar Morocco.

Baya ga haka kuma, ibtila’in ya dau wani salon siyasa yayin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da karbar taimakon jinkai daga kasashe kamar makwabciyarta kuma abokiyar hammayarta, Algeria, da kuma iyayen mulkin mallakarta Faransa, kana, ta amince da taimakon wasu tsirarun kasashe kawai. Masu suka sun ce hukumomi sun yi jan kafa wajen daukar mataki.

Sarkin Morocco Muhammad na BI yana birnin Paris a lokacin da girgizar kasar ta auku. Kwanaki bayan nan kuma ya ziyarci asibitoci dake biranen Marakesh da ibtila’in ya lalata.

Hukumomi sun kalubalanci sukar da ake musu sannan ‘yan Morocco sun bayyana martanin sakin da hukumomin kasar da girman kai. Kana sun nuna irin kayayyakin da aka taimaka musu da su kamar sutura, barguna, abinci da magunguna daga kasashe a fadin duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga
Kasashen Ketare

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Next Post
Wa’adin Da Tinubu Ya Bai Wa Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Ya Cika

Wa’adin Da Tinubu Ya Bai Wa Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Ya Cika

LABARAI MASU NASABA

Majalisar NUJ Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa

Majalisar NUJ Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa

October 22, 2025
Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11

Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11

October 22, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe

October 22, 2025
Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

October 22, 2025
An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

October 22, 2025
Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

October 22, 2025
Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

October 22, 2025
Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

October 22, 2025
Tanka

Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja

October 22, 2025
Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.