ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wa’adin Da Tinubu Ya Bai Wa Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Ya Cika

by Abubakar Abba
3 years ago
Tinubu

Wa’adin da Shugaba Kasa Bola Ahmad Tinubu, ya bai wa hukumomin tsaro na su karbo bashin Naira tirilayan 1.1, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba wa manoman shinkafa a karkashin shirin aikin noma na ‘Anchor Borrowers’, ya cika, amma shiru ka ke ji har yanzu wadannan manoma ba su maido kudaden ba.

Idan za a iya tunawa, Shugaba Tinubun ya umarci hukumomin su karbo wadannan zunzurutun kudade kafin ranar 18 ga watan Satumbar 2023 da muke ciki.

  • Xi Ya Karfafawa ‘Ya‘yan Wadanda Suka Sadaukar Da Rayuwarsu Da Su Zama Amintattu Masu Kare JKS Da Al’umma
  • Kaunar Da Xi Jinping Yake Nuna Wa Gari, Dangi Da Kuma Al’ummar Kasa

An bayar da wannan bashi ne domin kokarin sake habaka harkokin noma a Nijeriya tun a shekarar 2018. Koda-yake dai shirin ya samu nasarori a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, inda kuma ya samu tasgaro a wasu jihohin sakamakon kin biyan bashin da wasu daga cikin manoman shinkafar da suka amfana suka yi.

ADVERTISEMENT

Kazalika, an yi zargin cewa wasu daga cikin jami’an da aka dora wa nauyin bayar da bashin, sun karkatar da wani kaso daga cikin kudaden domin amfanin kawunansu.

Daga cikin wannnan adadi na Naira Tiriliyan 1.1 da aka bai wa  Manoman  Shinkafar, Naira biliyan 546 kacal aka iya maido wa. Amma, bisa wannan umarni da Shugaban Kasar ya bayar ne, ake sa ran manoman da suka ki biyan wadannan kudade da kuma sauran jami’an da aka dorawa nauyin karbo bashisshikan, suka karkatar da wani kaso daga ciki, za su maido da sama da Naira biliyan 577.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Muhimmancin Rungumar Kiwon Awaki A Tsakanin Matasa

Ƙungiyar KADCCAM Ta Jinjina Wa Hukumar Samar Da Abinci Ta FOA

Bugu da kari, wannan ya hada daruruwan manoman shinkafar da suka yi rijista da kungiyoyi aka ba su wannan rance, da ya hada da kayan aikin noma kamar takin zamani, magungunan feshi da sauransu.

Ana sa ran kuma manoman za su biya bashin ta hanyar bayar da wani bangare na amfanin da  suka girbe ko kuma ta hanyar biya da kudi lakadan.

Sai dai, karbo wannna bashi ya zamo wa Babban Bankin CBN wani babban kalubale ganin cewa, duk iya kokarin da aka yi na karbo bashin ta hanyar kungiyoyin manoman shinkafar, amma hakansu bai cimma ruwa ba.

Har ila yau, domin cika wannan umarni na Shugaba Tinubu, kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN), ta fitar da wata takarda mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Agustan 2023, inda ta umarci kafatanin rassan kungiyoyinta na jihohi da su yi aiki tare da jami’an tsaro domin karbo wannan bashi.

Sai dai, tun bayan wannan umarnin na RIFAN, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, bashin da aka karbo daga gun manoman da suka amfana a jihohin, bai taka kara ya karya ba.

Haka zalika, dalilan da suka janyo tarnaki wajen karbo wadannan bashisshika, kamar yadda Mataimakin Sakatare Janar na RIFAN din reshen Jihar Kano, Malam Ado Hassan, ya shelanta suna da daman gaske.

Hassan ya kara da cewa, kungiyar reshen jihar ta karbi bashin na kimanin Naira biliyan 12 daga 2017 zuwa  2020, amma bashin da ta iya karbo wa daga wurin wadannan manoma da suka amfana, bai wuce kaso 30 a cikin 100.

Sannan ya yi ikirarin cewa, a kakar noma ta 2018 ‘ya’yan kungiyar reshen jihar,  manoman shinkafa 44, 807 ne suka amfana a karkashin wannan shiri, duk kuwa da cewa sun fuskanci mummunar ambaliayar ruwan sama a wannan shekarar.

Ya ci gaba da cewa, a 2019 an fuskanci kalubalen Annobar Korona, wadda ba manoman shinkafa kadai ta shafa ba har da hada-hadar kasuwanci a fadin duniya baki-daya.

Sannan ya sake kokawa kan cewa, manoman shinkafar ba su samu wata diyya a kan asarar da suka yi ba, bayan afkuwar wannan annoba tare da kuma ta ambaliyar ruwan sama daga wurin Kamfanin Inshorar Aikin Noma na kasa (NAIC) ba.

Kazalika ya ce, a kungiyance an kai wannan rahoto kan afkuwar wannan annoba guda biyu, koda-yake an turo  Jami’an CBN da  na NAIC, zuwa gonakan manoman domin tantance asarar da suka tabka, amma shiru kake ji babu wani agaji ko tallafi da aka kawo musu.

Sannan sun bi hanyoyi da dama don karbo bashi, ciki har da yin amfani da sarakunan gargakiya, kotuna da sauran dabaru daban-daban, amma abin ya faskara.

Har ila yau, wani manomin shinkafa a Jihar Kano, Alhaji Ahmadu Usman ya yi nuni da cewa, zai wuya a iya karbo wadannan basussuka, domin kuwa ba hakikanin manoman da suka dace aka baiwa bashin ba, ‘yan siyasa aka bai wa suka yi san ransu.

Tinubu
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Muhimmancin Rungumar Kiwon Awaki A Tsakanin Matasa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ƙungiyar KADCCAM Ta Jinjina Wa Hukumar Samar Da Abinci Ta FOA
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Manoman Citta Sun Soki Gwamnatin Delta Kan Mayar Da Su Saniyar Ware

MASU ALAKA

Nazari Kan Muhimmancin Rungumar Kiwon Awaki A Tsakanin Matasa
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Muhimmancin Rungumar Kiwon Awaki A Tsakanin Matasa

June 20, 2026
Ƙungiyar KADCCAM Ta Jinjina Wa Hukumar Samar Da Abinci Ta FOA
Noma Da Kiwo

Ƙungiyar KADCCAM Ta Jinjina Wa Hukumar Samar Da Abinci Ta FOA

June 20, 2026
Kungiyar Manoman Citta Ta Kasa Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Tallafin Da Take Ba Su
Noma Da Kiwo

Manoman Citta Sun Soki Gwamnatin Delta Kan Mayar Da Su Saniyar Ware

June 19, 2026
Next Post
Kungiyoyin CONESAM Sun Baje Kolin Fasahar Sarrafa Kayan Amfanin Gona

Kungiyoyin CONESAM Sun Baje Kolin Fasahar Sarrafa Kayan Amfanin Gona

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.