Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lashe Premier League na bana na hudu a jere na shida a kaka bakwai na 10 jimilla bayan nasarar doke West Ham 3-1 a wasan karshe na mako na 38 da suka kara ranar Lahadi a Etihad.
Manchester City ta fara cin kwallo ta hannun ta Phil Foden a minti na biyu da fara wasan, kwallo ta shida da ya zura a raga a bana daga wajen yadi na 18 a kakar bana,
haka kuma shi ne ya kara ta biyu, sannan Rodri ya ci ta uku a wasan, sai West Ham ta zare daya ta hannun Mohammed Kudus saura minti uku su je hutun rabin lokaci.
- Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
- Ana Fargabar Shigo Da Shinkafar Da Ta Jima A Ajiye Daga Thailand
Manchester City ta zama ta farko da ta lashe Premier League na hudu a jere, kuma na shida cikin kaka bakwai a tarihin babbar gasar ta Ingila shekara 135, sannan kungiyar ta lashe kofin bayan wasa 44 a jere a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa da cin wasanni 37 da canjaras bakwai.
Pep Guardiola ya lashe kofin lig na 12 a kaka 15 a matakin koci, mai uku a Barcelona da uku a Bayern Munich da shida a Manchester City wanda babu wani koci da ya hada wannan tarihi cikin ‘yan shekaru marasa yawa.
Dan wasa Erling Haaland ya ci kwallo 64 a wasa 66 a Premier League shi ne kan gaba a wannan bajintar a kaka biyu da ya fara buga babbar gasar Ingila, sannan ya lashe takalmin zinare karo biyu a jere da kwallo 27 a raga, wanda ya zura 36 a bara a Premier League.
Dan wasan Sifaniya, Rodri, ya yi wasanni 74 ba tare da an doke Manchester City ba, inda aka ci karawa 58 da shi da canjaras 16, tun bayan da Tottenham ta ci 1-0 a cikin Fabrairun 2023.
Manchester City ta buga wasanni 38 da cin 28 da canjaras 7 da rashin nasara uku da cin kwallo 96 aka zura mata 34 da maki 91 kuma dan wasa Phil Foden ne gwarzon dan wasan Premier League na bana, wanda marubuta labarin wasan kwallon kafa suka zaba a bana.
Foden ya lashe kyautar wanda ya ci kwallo 19 ya bayar da takwas aka zura a raga a babbar gasar ta bana, sannan Manchester City ce kan gaba a yawan cin wasan Premier League, wadda ta yi nasara 28, sai Arsenal ta biyu mai cin karawa 28 da kuma Liberpool mai 24.
Wannan shi ne Premier League na 10 jimilla da Manchester City ta lashe. Wadanda ke kan gaba a yawan lashe Premier League;
Manchester United 20. Liberpool 19. Arsenal 13. Manchester City 9. Eberton 9. Aston Billa 7. Chelsea 6. Sunderland 6. Sheffield Wednesday 4. Newcastle United 4. Blackburn Robers 3. Leeds United 3. Wolberhampton 3. Huddersfield Town 3. Derby County 2. Tottenham 2. Burnley 2. Portsmouth 2. Preston North End 2. Leicester City 1
Nottingham Forest FC 1. Ipswich Town 1. West Bromwich Albion 1. Sheffield United 1