Shugaban kungiyar fina-finai ta kudancin Nijeriya (Nollywood), Emeka Rollas, ya bayar da cikakken bayani kan yadda aka yi garkuwa da wasu jarumai; Cynthia Okereke da Clemson Cornel.
A cewar shugaban kungiyar, masu garkuwa da Okereke da Cornel sun bukaci a biya su kudin fansa dala 100,000.
“Sun kira waya suna neman kudin fansa $100,000,” in ji Rollas.
Idan za a iya tunawa, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatariyar kungiyar, Monalisa Chinda-Coker, ta bayyana cewa an yi zargin cewa an yi garkuwa da jaruman biyu ne a ranar Juma’a.
Rollas, ya bayyana a wata sanarwa cewa, “Ba mu tabbatar da sace su ba.
“Muna sa ran samun wata alama daga mutanen da suka yi garkuwa da su don sanin ko sace su ba a sace su ba.”
Sanarwar da Chinda-Coker ta fitar da farko ta ce, “An zargi jaruman biyu an yi garkuwa da su, lamarin da ya kara fargabar mambobin kungiyar game da tsaron lafiyar jarumai kasar.
“Saboda wannan abin bakin ciki ne, shugaban kungiyar na kasa, Ejezie Emeka Rollas, ya umarci dukkan ’yan fim da su guji zuwa wasu birane don yin fim, sai dai an samar da cikakken tsaro don tabbatar da tsaron lafiyarsu.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Cynthia Okereke da Clemson Cornell an yi fargabar garkuwa da su ne bayan da suka bar wajen wani daukar fim a jihar Enugu ranar Juma’a.
A cewar Monalisa Chinda, an ba da rahoton cewa tsofaffin jaruman sun bace ne bayan da ’yan uwansu suka tabbatar da cewa ba su dawo daga wurin fim ba a Garin Ozalla, Jihar Enugu.
Rollas ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan uwa da su yi addu’ar Ubangiji ya kubutar da abokan aikin nasu.