A makon da ya gabata hotuna da ma bidiyoyi suka yadu a kafafen sada zumunta musamman manhajar Facebook inda aka ga babban mataimki na musamman akan harkokin nishadi na gwamnan Jihar Kano Malam Tijjani Gandu ya na raba makullan mota da kudade ga wasu daga cikin jarumai a masana’antar Kannywood.
Kamar yadda aka gani a cikin faifan bidiyon an ga Tijjani ya na mika makullan mota ga jaruman tare da leda wadda ya ce ta na dauke da kudaden da za su yi amfani da su wajen sayen man fetur da kuma yi wa motocin rijista da hukumar kiyayaye hadurra ta Nijeriya, inda kuma ya ce wannan kyauta ce daga Gwamnan Jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya ce abasu domin nuna godiya a kan jajircewarsu a lokacin yakin neman zaben jihar Kano da aka gudanar a shekarar 2023.
- Sakon Da Aka Isar Game Da Yanayin Tekun Kudancin Kasar Sin Daga Wasu Taruka Uku
- Xi Ya Bukaci A Yi Kokarin Tafiyar Da Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Yadda Ya Kamata
Yayin da wasu ke fita daga tsagin Kwankwasiyya na siyasar Jihar Kano su na komawa tsagin APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin (Maliya) su kuma wadanda suka jure suka tsaya a jam’iyar NNPP mai alamar littafi suke rabauta da kyaututtukan manyan motoci masu tsada da kuma kudade daga gwamnatin jihar ta Kano, inda babban mai taimakawa gwamnan akan harkokin nishadi Malam Tijjani Gandu ya ce gwamnan ya matukar yaba wa da irin gudunmawar da jaruman suka ba shi a lokacin da yake yakin neman zaben gwamna.
Hakan ya sa gwamnan ya yi amfani da kalmar bahaushe da ta ce yaba kyauta tukwuici, ta hanyar gwangwaje wasu daga cikin jarumai mata da maza da motoci da kuma kudaden shan mai, Tijjani kuma ya tabbatar da cewar wannan somin tabi ne domin kuwa gwamna Abba Kabir Yusuf ya na sane da wadanda suka samu da wadanda basu samu ba,da sannu sanu duk wanda ya cancanci samun kyautar mota daga hanun gwamnan za ta shigo hannunshi inji shi.
Leadership Hausa ta kalato maku sunayen jaruman Kannywood da suka samu wannan kyauta ta mota daga gwamnan Jihar Kano Eng Abba Kabir Yusuf ta hannun babban mai taimaka masa akan harkokin nishadi Malam Tijjani Gandu, ga sunayen kamar haka, Alasan Kwalle, Bashir Nayaya, Baba Sogiji, Isiyaku Jalingo a bangaren maza sai kuma Ainau Ade da Yahanasu Sani a bangaren mata.