Bayan da kasashen Birtaniya da Canada da kuma Australia suka shiga jerin wadanda suka amince da kafuwar kasar Falasdinawa, ana sa rana wasu kasashen su ma su bi sahu.
To amma yaya kasashen Afirka ke kallon batun kafuwar kasar Falasdinawa?
- Me Ya Sa Kamfanonin Jamus Fiye Da 560 Suka Zabi Wani Gari A Kasar Sin Don Gudanar Da Harkokinsu?
- Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A KuÉ—in Naira
Akasarin kasashen Afirka sun amince da kafuwar kasar Falasdinawa tun a shekarun 1980 bayan da bayan da jagoran Falasdinawa Yasser Arafat ya ayyana ‘‘yancin kan yankin a birnin Algiers.
Shugabanni irin su Thomas Sankara da Nelson Mandela duk sun alakanta fafutukar neman ‘‘yancin Falasdinawa da fafutikar kasashen Afirka na samun ‘‘yanci.
Sai dai, kasashe biyu – Kamaru da Eritrea – ba su yi hakan ba.
Kamaru
Kasar Kamaru tana da alaka sosai da Isra’ila.
Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Kasashen Afirka da tsare-tsare a Geneba, Dabid Otto ya ce Isra’ila na kallon Kamaru a matsayin daya daga cikin kawayenta na kusa a Afirka.
Ya ce “Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alakar diflomasiyya da ke tsakaninta da Isra’ila ba.”
Ya ce alakarsu na da kwari sosai, kuma ya shafi batu ne na tsaro.
“Isra’ila ta taimaka sosai kuma tana ci gaba da taimakawa wajen kare gwamnatin Kamaru,” in ji shi.
Isra’ila ta bayar da horo, kuma ana da amannar cewa tana ci gaba da bai wa dakaru na musamman na Kamaru horo, wani abu da ke tabbatar da tsaron shugaban kasar.
“Haka nan kuma kyakkyawar alakar da ke tsakanin Kamru da Isra’ila ta sanya Kamaru din tana samun goyon baya daga Amurka ta bayan fage.”
Haka nan kuma matsayar Kamaru game da yankin Falasdinawa, akwai yiwuwar yana da alaka da artabun da take yi da ‘‘yan aware na yankin da aka fi amfani da harshen Turanci a kasar.
“Amincewa da kasar Falasdinawa zai iya haifar da karin matsi a cikin kasar, wanda hakan zai alamta cewa su ma masu fafutikar kwatar ‘yancin kai na kasar, su ma suna da hujja ke nan. Bayan kuwa Kamaru ta nanata cewa ita kasa daya ce wadda ba za ta balle ba,” in ji Otto.
A yancin lokaci Kamaru na kame bakinta ne kawai a duk lokacin da ake magana kan amincewa da kafa kasar Falasdinawa.
Ita kuwa Eritrea, tata matsayar na da dalilai da suka sha bamban, wadanda suka samo asali daga tata fafutikar ta samun ‘‘yanci.
Eritrea
A shekarar 1988 lokacin da Yasser Arafat ya ayyana ‘yancin kasar Falasdinawa, yana bukatar goyon bayan kasashen Afirka.
Daya daga cikin wadannan kasashen ita ce Ethiopia, wadda ita ce ke da mazaunin cibiyar Kungiyar Hadin kan Kasashen Afirka a wancan lokacin, wadda daga baya ta koma Tarayyar Afirka, a birnin Addis Ababa,” in ji mai sharhi kan siyasa dan kasar Ehiopia, Abdurahman Sayed.
“Gwamnatin mulkin soji ta wancan lokacin tana kuma goyon bayan Tarayyar Sobiet, saboda haka tana goyon bayan ‘‘yanci da kuma hakkin Falasdinawa.”
To amma a lokacin ita kuma Eritrea tana fafutikar neman ‘‘yancinta daga Habasha.
“A bayyane yake cewa a wancan lokacin Habasha ta mamaye Eritrea. Kuma a lokacin ‘‘yan Eritrea sun dauki makamai suna neman kwatar ‘‘yancin kansu daga Habasha,” in ji Sayed.
“A lokacin idan har Falasdinawa na son yin kyakkyawar alaka da Ethiopia to dole ne su nesanta kansu daga Eritrea, kuma ina ganin abin da Yasser Arafat ya yi ke nan, lamarin da bai yi wa ‘yan Eritrea dadi ba, ciki har da shugaban Eritrea na yanzu,” in ji shi.
Sai dai duk da haka, shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya nuna tausayawa ga Falasdinawa, a 2012 ma ya kada kuri’ar amincewa da bai wa yankin Falasdinawa matsayin “mai sa ido” a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai kuma ya yi watsi da tattaunawar zaman lafiya ta Oslo, wadda ta samar da tsarin zaman lafiya da ya bai wa Falasdinawa kwarya-kwaryar ‘‘yancin kai a wani yankin Gabar Yamma da Gaza, a matsayin wani mataki na samun ‘‘yancin kai.
“Shugaban Eritrea na daga cikin na farko-farko da suka yi watsi da yarjejeniyar Oslo a 1993, inda ya bayyana ta a matsayin maras amfani wadda ba za ta taimaka wajen warware rikicin da ake fama da shi ba ko kuma hankoron yankin na samun ‘‘yancin yankin Falasdinawa,” in ji Abdurahman Sayed.
Shugaba Afwerki ya ce ba ya goyon bayan kafa kasa biyu.
To sai dai zai iya fuskantar matsi daga cikin gida kasancewar kashi 55 cikin dari na al’ummar kasar Musulmai ne.
“Eritrea ta samu nasara a fafutukarta ta samun ‘‘yanci. Saboda haka a ce mutumin da ya jagoranci fafutikar samun ‘‘yanci kuma ba ya goyon bayan wasu su samu ‘‘yanci, za a ga kamar hakan ba abu ne mai kyau ba. Za su fuskanci matsi,” in ji Sayed.
BBC ta nemi jin ta-bakin gwamnatocin kasashen biyu, amma ba su bayar da amsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp