Gwaman Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa; gwamnatinsa za Ta kaddamar da babban shirin aikin noma, wanda zai taimaka wa farfado da aikin noman na bana a fadin jihar, don kara samar da wadatacen abinci da kuma magance kalubalen rashin tsaro a jihar.
Buni ya kara da cewa, manufar shirin shi ne; don kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasan jihar domin inganta rayuwarsu ta gobe.
- CMG Ya Kaddamar Shirin Musayar Al’adun Abinci Na Sin Da Faransa
- Dalibai Miliyan 1.4 Da Suka Rubuta Jarra-bawar UTME Sun Ci Maki Kasa Da 200
Gwamnan ya bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da hadiminsa na yada labarai, Mamman Mohammed ya bayar.
Kazalika, ya bukaci matasan jihar da su yi kokarin amfani da wannan dama, don kara fadada aikin noma a yankunan nasu.
Acewar tasa, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen bunkasa aikin noma, musamman ganin yadda manoman jihar za su amfana da samun dimbin kudaden shiga.