• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wadda Ta Sha Ingiza Matsalolin Abinci A Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Wadda Ta Sha Ingiza Matsalolin Abinci A Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar kula da shirin abinci ta MDD (WFP) ta yi gargadi a kwanan baya cewa, ‘yan Adam ka iya fuskantar “matsalar abinci mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu”. Matsalar kuma ta fi yin tasiri ga kasashen Afirka.

Hauhawar farashin abinci a sakamakon matsalar karancin abinci na matukar addabar al’umma, musamman na kasashen da ke fama da rashin ci gaba.

  • Asarar Da Ukraine Ke Tafkawa Duk Wata A Yakinta Da Rasha

Amma kuma manyan kamfanonin hada hadar cinikin abinci na duniya na cin muguwar riba sabo da matsalar. Daga cikin manyan kamfanonin cinikin abinci mafiya girma guda hudu na duniya, wadanda ke shafar kimanin kaso 75% zuwa 90% na cinikin abinci na duniya, akwai guda uku da suka kasance na kasar Amurka, wadanda suka hada da ADM da Bunge da Cargill.

Sai dai sakamakon matsalar karancin abinci da hauhawar farashinsa, akwai mutane uku ‘yan gidan masu kamfanin Cargill da kadarorinsu suka karu da kimanin kaso 20% a wannan shekara, lamarin da ya sa suka shiga jerin mutane 500 mafi arziki a duniya. Baya ga haka, sauran kamfanonin biyu sun samu matukar hauhawar farashin hannayen jarinsu.

Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Henry Alfred Kissinger ya taba cewa, “Wanda ya mallaki man fetur, ya mallaki kasashen duniya, kuma wanda ya samu iko a kan takardun kudi, ya samu iko a kan tattalin arzikin duniya, yayin da kuma wanda ya mallaki abinci, ya samu iko a kan ‘yan Adam.”

Labarai Masu Nasaba

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

A hakika, ana iya gano hannun Amurka a matsalolin karancin abinci da aka fuskanta a tarihi. Ta hanyar ingiza abin da ake kira wai “ciniki mai ‘yanci”, da kuma fitar da irin da aka kirkiro wadanda ba su iya haiyayyafa ba da kuma fasahohin noma na musamman, Amurka ta lalata tushen aikin noma na kasashe a tasowa, wadanda har suka kasa dogara da kansu, tare da kara dogara da ita wajen samar da abinci.

Ta hakan kuwa, Amurka ta samu iko a kan farashin abinci na duniya har da tsarin samar da abincin, kuma ta yi babakere a wannan fanni. (Mai zane: Mustapha Bulama)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Buhari Ya Ja Kunnen Matasa: Ku Nemi Ilimi Ba Don Aikin Gwamnati Ba Kawai

Next Post

Tinubu Ya Yi Daidai Da Ya Zabi Musulmi Mataimaki – Oshiomhole

Related

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 
Daga Birnin Sin

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

16 hours ago
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

17 hours ago
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 
Daga Birnin Sin

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

18 hours ago
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

19 hours ago
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

20 hours ago
CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu
Daga Birnin Sin

CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu

2 days ago
Next Post
2023: Tinubu Ya Zaɓi Kashim Shettima A Matsayin Mataimaki

Tinubu Ya Yi Daidai Da Ya Zabi Musulmi Mataimaki - Oshiomhole

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta

Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta

August 25, 2025
Ƙungiyar KSCI Ta Nemi Sabon Tsari Don Magance Ƴan Bindiga A Katsina

Ƙungiyar KSCI Ta Nemi Sabon Tsari Don Magance Ƴan Bindiga A Katsina

August 25, 2025
Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kano

Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kano

August 25, 2025
Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

August 25, 2025

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.