Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999 a Nijeriya, an taɓa sanya dokar ta-ɓaci a wata jiha sau ɗaya kacal.
A ranar 18 ga watan Mayu, 2004, a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo, an ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Filato.
- Dabarun Kasar Sin Na Iya Kawo Karshen Yunwa A Duniya
- EFCC Ta Ƙwato Naira Biliyan 365.4 A Shekarar 2024
Wannan mataki ya sa aka dakatar da Gwamna Joshua Dariye da ‘yan majalisar dokokin jihar.
Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000.
A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba
A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram.
A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro.
Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya.
Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci da matsalolin tafiyar da gwamnati.
Shugaban Ƙasa Yana Da Dama Bisa Doka
Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa Shugaban Ƙasa damar ayyana dokar ta-ɓaci a wata jiha idan ana fuskantar matsalar tsaro ko rikicin shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp