Ƙudurin tsarin mulkin Nijeriya shi ne tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaba wanda yake daya ne daga cikin tsarinta na hulda da kasashen waje idan aka yi la’akari da hakan a matsayin sahihiyar kudurin neman zave, in ji Ministan Harkokin kasashen Waje Hon. Yusuf Tuggar.
An haife ni a lokacinda ake yakin basasa don haka ban samu damar zaven shugabanni na ba, sai da na kai shekara 30 da haihuwa. Yanzu ana tafiyar da mulkin kasar nan ne bisa doka da kuma tsarin mulki wanda ya fayyace tsarin tafiyar da gwamnati. Wannan tsari ya hada da manufofin tsarinta na hulda da kasashen waje, saboda wannan tsari na game-duniya, muna ayyana matsayinmu na ’yantacciyar kasa ta fuskar wasu muhimman ka’idoji wadanda suka hada da tabbatar da ‘yancin cin gashin kanmu da kuma kare iyakokin kasarmu da kuma girmama alkawuranmu karkashin dokokin kasa da kasa.
- Ministan Wajen Sin Ya Tayawa Takwaransa Na Najeriya Murnar Kama Aiki Ta Wayar Tarho
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Lashi Takobin Karfafa Hadin Gwiwa Da Afirka
A matsayina na Ministan harkokin kasashen waje, ina ganin wadannan tanade tanaden ba wai kawai dacewa kawai suka yi ba, sun kasance muhimman ginshikai ne wajen tabbatar da dimukuradiyarmu, zaman lafiya a cikin-gida Nijeriya da kuma wadata, har ma da adalci da kuma daidato a zaman lafiyar duniya, amma muhimmin batu a nan shi ne, tsarin mulkin Nijeriya ne ba kudurin wata jam’iya ba, ko ra’ayin da wani dan siyaysa ya gabatar ba, a tsarin dimukuradiya muna da alfarmar gudanar da muhawara cikin lumana dangane da akidinmu tsare-tsarenmu da kuma kokarin da muke yin a aiwatar da tsare-tsarenmu. Amma idan muna so mu sauke alhakin da yake kanmu wanda yake zuwa tare da tsarin mulkin dimukuradiya inda ya kamata a gudanar da muhawarar ne bisa sani da dattaku da kuma adalci.
Ina girmama tsarin mulkinmu saboda hangen nesarta na nemawa Nijeriya muhimmin matsayi a kasashen duniya, kamar yadda da yawanmu masu irin wannan ra’ayi suke dubanta. Dama ce mai girma da kuma karimci a gare ni wajen kare da kuma kawo ci gaban wadannan akidu na tsarin mulki. Su ne tabbaci na halacci da kuma iko da kowace gwamnati ke bukata idan suna so yi nasara. Wannan hanya na da sarkakiya da kuma daukan lokaci.
Yau da gobe sun koya mana cewa, babu wata hanya mai sauki ga samun nasara. Wasu ‘yan Nijeriya suna so aibanta tsarin mulkinmu, wasu ko suna so su yi mashi gyaran fuska. Tsarin mulkin dimukuradiya na bayar da damar gudanar da muhawara cikin lumana . Amma a zahiri, magana ta gaskiya ita ce, kundin da shugabana kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma duk wani mai rike da mukami suka yi rantsuwar karewa da kuma daukakawa tun 1999.
Tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana cewa ‘yancin mulkin kai na hannun jama’ar kasa ne, wanda gwamnati ta hanyar kundin tsarin mulki ta samu karfinta da ikonta. Tsarin mulkin kasa ya bayyana manufofin hulda da kasashen waje guda biyar wadanda suka hada da: gabatarwa da kuma kare muradun kasa, hada kan kasashen Afirka da kuma taka rawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da girmama juna, da kuma girmama dokokin kasa da kasa da girmama alkaura da tabbatar da adalci a duniya da kuma samar da tsari a tattalin arzikin duniya.
Wadanda suke tunanin cewa Nijeriya ba ta da tsarin hulda da kasashen waje, ko wadanda suke yayata bukatar cewa Nijeriya ta sauya tsarinta na fifita harkokin hulda da kasashen Afirka a cikin tsarin huldarta da kasashen wajenta sun yi kuskure ko kuma ba su da wadatacciyar masaniya a kan batun, ko kuma da ganagar suke murde batu don son zuciya.
Abin lura a nan shi ne ‘yan Nijeriya suna iya tofa albarkacin bakinsu wajen nuna goyon baya ga mulkin soja da ake yi a kasashe makwabtanmu da kuma tafiyar da mulkin kasashen ba tare da tsarin mulki ba, wannan yana yiwuwa ne saboda babi na hudu na tsarin mulkinmu ya ba su ‘yancin yin haka. Wannan damar ba ta samuwa ga ‘yan wasu kasashen da sojoji ki mulki ba tare da tsarin mulki ba.
‘Yan Nijeriya wadanda suka zarce shekara 30 da haihuwa sun san cewa wannan gaskiya ce saboda mun fuskanci hakan. Yau da gobe ya sa wasu sun manta cewa, mulkin soja da aike sojoji zuwa kasashen Sierra Leone da Liberiya a shekarun 1990 dan tabbatar da mulkin dimukuradiya an yi su ne ta hanyar savawa tsarin dimukuradiya ta hanyar karve mulki da karfin soja, sa’annan suka kwace tsarin dimukuradiya da mulkin doka daga hannunmu kamar yadda wasu gwamnatocin mulkin soja suke yi a sassa daban-daban na duniya.
Tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana karara dalilin da zai sa duk wani gwamnati dake cikin hayyacinsa, ba zai damu ba, a duk lokacinda makwabtansa ke tafiyar da harkokinsu ba bisa tsarin mulki ko wata ayyananniyar doka ba. Ana iya cewa ‘yancin kan makwabtanmu abinda ya shafe su ne, suna iya bada ikon tafiyar da kasarsu ga kowani tsari na tafiyarda mulkin da suke so, kuma su tsammaci wannan gwamnatin za ta kare musu ‘yancinsu. Amma da zaran ‘yancin mulkin kanmu ya zovara kan iyakokinmu muna da dama da zamu yi amfani da ikonmu a kan iyakokinmu a yaninda makwabtanmu suke fama da ‘yan tada kayar baya wadanda suke kwance tukkar kokarinmu na tabbatar da ‘yancin cin gashin kanmu da kuma zama ‘yantacciyar kasa.
‘Yancin kai a tsarin shari’ar kasa da kasa na zama wani batu idan muka yi la’akari da cewa girmama dokar kasa da kasa da kuma girmama alhakin yarjejeniya na daya daga cikin muhimman manufofin tsarin hulda da kasashen wajen Nijeriya. Wannan ba tsarin hulda da kasahen waje na gwamnatin Tinubu ba ne tanadi ne na tsarin mulki da kowani shugaban Nijeriya da ma’ikatan gwamnti suka yi rantsuwar tabbatar da shi.
Nijeriya memba ce ta kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS), wacce aka samar da ita bisa yarjeniyoyi wanda tsare-tsare da manufofin hulda da kasahen waje na kasa ya tabbatar mana. Duk kasashe 15 na kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma,(ECOWAS), sun rataba hanu akan wannan yarjeniyoyi saboda haka ba.
Tinubu a matsayin wanda ya lashi tokobin girmama tanadin tsarin mulki a lokacinda daukacin shuwagabanin kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma,(ECOWAS) suka nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin soja.
A zahiri, tsarin tafiyar da kasashe a wannan zamani yana da matukar sarkakiya, kuma Nijeriya ta kasance ne a wata duniya na kowa ta kansa yake. Tsarin mulkinmu da dokar kasa da kasa an yi su ne domin su zama linzamin hulda tsanin kasashen duniya. Idan muka yi la’akari da girmanmu a cikin kasashen Afirka zamu fahimci cewa muna da wani karin nauyi a kan mu, na zama jagorar kasashe a nahiyar Afirka ba tare da damuwa da yadda wasu zasu dubi matsayin namu ba.
Tsarin mulkinmu ya kara karfafa rawar da muke takawa a matsayin jagora tun daga gabatarwarsa inda ya nuna sadaukarwarmu ga tabbatar da zumunta tsakanin kasashen Afirka, manufofin tsarin hulda da kasashen ya nuna fifikon da muke da shi wajen hada kan Afirka da kuma kawar da duk wan inau’in nuna wariya.
Wannan mulki na shugaba Tinubu ya zo ne a wani lokaci da ake samun aukuwar al’amura wadanda suka sa yankinmu ke fama da matsalar tsaro; tun daga kasar Libya da kuma gazawar shirin kasashen Turai (EU) a yankin Sahel da ta’addanci, da ayyukan gungun masu aikata laifuka da tasirin canjin yanayi da karuwar yawan jama’a a duniya. Nijeriya ba ta kirkiri wadannan matsalolin da muka ambato ba, hasali ma tana fama da irin nata matsalolin cikin gida a yayinda wadannan kalubalen suke karuwa.
Ita Nijeriya ba ta daga cikin Gangamin Barkhane ko kuma Tarayyar karfafan kasashe 5 na yankin Sahel, wadanda suke da zimmar yakar ta’addanci da kwararar bakin haure mara ka’ida maimakon karfafa wa Buzaye ko Azibinawa masu kula da kan iyakoki gwiwa. Rashin hakan, ya haifar da rashin jituwa tsakaninsu da sojojin kasar wadanda aka dauke su dindindin to kare kasashen nasu.
Haka kuma, Nijeriya ba ta kasance cikin kawancen kasashen masu tasowa ba wadanda, suka tsara taimakekeniya ba, kuma ba su kulla huldar kasuwanci da su ba, wanda zai taimaka wa masu kaura a yankin Sahel na shige da fice a cikin kasashen don rage kwararowar bakin haure, tare da hukunta duk wadanda suka karya doka.
Game da Jumhuriyar Nijar kuwa, an samar da wata doka mai lamba 2015 – 36 a shekara ta 2015 bayan gwaunatin kasar ta kammala tuntuvar Ofishin Majalisar dinkin Duniya a kan Miyagun kwayoyi da Manyan Laifuka, tare da taimakon kwararru game da tallafin na kudi daga Tarayyar Turai da kawayenta, inda suka ayyana haramcin wasu ayukkan bakin hauren, kamar tanada wa bakin ketare sufuri don yi musu jigila da ba su masaukai a fadin Arewacin Agadez, wannan ya sava wa yarjejeniyar kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS) wanda ya halatta walwalar jama’a a ko’ina.
Ana matukar kokarin wajen shawo kan matsalar. Matsalar bakin haure a wani sashe na kasashen Turai ta siyasance. Lallai ya kamata a magance matsalar bai daya. Ba zai yi ma’ana ba, a ce an magance wata matsar ta hanyar haifar da wata.
Ba haka kawai ake da tsarin walwala na shige da fice a Yammacin Afirka ba. Tafiya ci-rani da ake yi duk shekara a yankunan saimon Hamadar Sahel babban al’amari ne da ake yi bakin rai bakin fama. Wannan ne dalilin da ya sa, Buzu daure da rawaninsa zai iya tafiya mai nisa har Legas ko Fatakwal don ya yi aiki gadi a lokacin rani, da zarar damina ta sauka sai ya koma gida.
Tun da yankin hamadar Sahara ya zama matattara ta hada-hadar muggan makamai daga kasashen Turai, kuma aka riki hakan a matsayin hujjar siyasar sama wa yankin Sahel din tsaro, sai akasin haka aka samu. Don tsaron ya kara tavarvarewa. An kai matsayin da wadanda matsalar tsaron ta fi shafa, suna aukawa cikin ayukkan ta’addanci don tsananin kuncin rayuwa. Hukumar bakin haure ta Turai ta nuna mafi yawan bakin hauren, ‘yan gudun hijira ne daga kasar Siriya da Afghanistan da Tsakiyar Asiya amma ba yankin Saharar Afurka ba.
Lallai ya kamata mu yi aiki tare da makwabtanmu na yankin hamadar Sahel don hada karfi da karfe a yaki ta’addanci, ta hanyar amfani da hanyar da ta dace da yankunan juna.
Idan ana so a cim ma dawwamammen zaman lafiya a kasar Libiya da yankin Sahel, to dole ne Nijeriya ta hada kai da sauran makwabtanta da sauran kasashen masu karfi. Don haka, ba hikima a ce Nijeriya ta ware kanta, ta nisanta kanta daga kasar Faransa, don kawai kasashen da ta mulka sun bijire mata, kamar yadda ya auku.
‘Yantacciyar Mafita’ ita ce ginshikin dokar kasa da kasa a mulkin Shugaba Tinubu. Za ta ba mu damar kulla alaka bayyananniya da duk wata kasa gwargwadon muradun kasarmu ba don wasu ba. Yanzu fa, Nijeriya ta riga ta kawo karfi kuma ta girmama ta yadda za ta iya mu’amala da sauran kasashen ba tare da tunanin a juya ta yadda ake so ba, ko ake zato. Barin kashi a ciki, ba ya maganin yunwa dai.
Nijeriya da kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS) za su ci gaba da huldarsu ta diflomasiyya don shawo kan kasar Nijar da kasar Mali da kasar Burkina Faso. A takaice dai, akwai zumunci da mutuntawa a tsakaninmu har yanzu. Shugaba Tinubu ya aike da manyan wakilai, ciki har da mai girma tsohon shugaban kasa, tare da Sarakuna da malaman addini don tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban kasa Tinu, ya yi namijin kokari, inda ya bukaci a janye takunkumin da aka kakaba wa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso. Abin da shugaba Tinubu ya fi jaddada wa masu kakaba takunkumin, shi ne, su fi mayar da hankali a kan shirin mayar da mulki a hannun farar hula. Game da kasar Nijar kuwa, ya fi damuwa da batun hamvararren shugaban kasar, Shugaba Bazoum.
Sai dai, su a nasu vangaren, sun mayar da murtani da cewa, za su fice daga kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS). Sun bayar da sanarwar wa’adin shekara daya na ficewar, wanda zai cika a karshen watan Janairun 2025. Shugaba Tinubu ya kara matsa wa kungiyar Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS) lamba da ta kara wa’adin da kamar wata shida; yayin da yake ta kokarin sasanci a diflomasiyyance. Game da zarge-zarge, a watan jiya, an samu kwaranyewar duk zargi game da rade-radin cewar Nijeriya za ta saukar da bakin sojoji daga kasashen waje da nufin tallafa wa ta’addanci a kasar.
A duk lokacin da mai girma shugaban kasa tare da mashawarta a harkar siyasa suka kaddamar da wani tsari da ya shafi hakuri da juriya, da hadin kai don neman mafita har a cim ma buri; sai wasu su karkatar da manufar a matsayin gazawar gwaunati wajen magance wasu matsaloli a aikace. Lallai wannan ne dalilin da ya sa ake cewa: “Munafikinka, tabarmarka.”
Ni a nawa vangaren, tun da na hau wannan mukamin na Ministan Harkokin Waje ranar 21ga Agusta, 2023, ban yi kasa a gwiwa ba, ina mai kai-komo tare da gayyatar manyan jami’an gwaunati da wakilai don yaukaka huldar diflomasiyya. An samu sakamako mai armashi na diflomasiyya zuwa yanzu.
Mun kafa kwamiti na shawarwari karkashin ofishin minista wadanda suka ziyarci kasar Nijar da Mali. Kuma mu muka shirya ziyarar manyan hafsosinmu “CDS” inda suka gana da abokan aikinsu na kasar Nijar a birnin Niamey. Sai dai, ban ji dadin soke ziyara ta biyu da hukumomin Nijar din suka yi ba, alhalin har an tsayar da rana da lokaci. Amma, ba haufi, za mu ci gaba da bibiyarsu cikin lalama ta amfani da ofishin ministan harkokin waje wanda ya yi shekar 67 da kafuwa.
Shirin ‘Yantacciyar Manufa’ ta Nijeriya yana daga cikin mafi kyamatuwar shiri, ya fi kyamar girke dakarun kasashen waje ko kuma kamfanoni sojojin haya a cikin yankinmu, ya’alla Gabas ne ko Yamma. Ko a yanzu, muna da sojoji da suka je aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Guinea Bissau da kasar Gambiya, ga wasu can a hanyar zuwa kasar Sierra Leone, sannan kuma, ana nan ana shirin samar da sansanin jaura a yankin Lungi.
Nijeriya ita ce kan gaba wajen tabbatar da kafuwar sojojin ko-ta-kwana, ta kungiyar kasuwanci ta Yammacin Afurka ‘ECOWAS’ duka dai a kan kokarin yakar ta’addanci da tashin tashina a yankinmu kamar yadda doka ta tanada. Muna aiki da ‘yan uwanmu wajen musayar bayanan sirri domin samun cikakkiyar walwala, ‘yanci da lumana ga duk mahalukin da ke yankin.
Kamar yaddda abokan aikina na yankin ke tuna mini, cewar mu ne gavaren, ko mun yarda, ko ba mu yarda ba. Kamar haka, siyasar duniya take, kamar kimiyya ce, tarawa da debewa, jerin tsari, yaduwar kuzari, daidaito da sauransu. Nijeriya ba ta tava tunanin mamayar wata makwabciyarta ba, ko kuma a yi mata barazanar mamaya. A kowane lokaci, Nijeriya ta fi zabar zaman lumana tare da sulhu.
Wannan kadan ne daga cikin tsare-tsarenmu da suka shafi Hukuma da harkokin al’umma. A matsayinta ta babbar kasa, mun saba da mutuntawa da kawar da kai. Mun yi matukar sa’a, don da wuya a samu kasa da ke da tsofaffin shugabanninta har guda shida, kuma duka suna nan cikin zaman lafiya da fahimtar juna. Kasancewarmu nau’i-nau’i ba yana nufin savani ba ne, nuni ne ga karfi. Haka yake ga Nijeriya, za ta tsaya wa karamar kasa; kuma ita ta kowa ce a wannan yankin.
Tuggar shi ne Ministan Harkokin kasashen Waje na Tarayyar Nijeriya. -7 ga Janairun 2025