Sakatarorin tsaron Amurka da na Rasha sun tattauna ta wayar tarho, a wani yunkuri na ba kasafai ake mu’amala ba tsakanin kasashen biyu tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.
Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin da takwaransa na Rasha Sergei Shoigu sun gana ne a ranar Juma’a, kamar yadda kasashen biyu suka tabbatar.
- Bukatar Kawo Karshen Rushewar Gine-gine A Nijeriya (Ra’ayinmu)
- DA DUMI-DUMI: An Sanya Wa ‘Yan Nijeriya Dokar Hana Samun Izinin Shiga Dubai
Bangarorin biyu sun ce an tattauna ne kan halin da ake ciki a Ukraine.
Wannan dai shi ne karo na farko da kasashen biyu suka bayar da bayanin wata tattaunawa tun ranar 13 ga Mayu 2022.
Bayan tattaunawar ta ranar Juma’a, ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Mista Austin “ya jaddada muhimmancin kiyaye layukan sadarwa a Ukraine”.
Ma’aikatar tsaron Rasha kuwa ta ce “an tattauna batutuwan da suka shafi tsaron kasa da kasa ciki har da halin da ake ciki a Ukraine”.
Bayan tattaunawar da suka yi a baya a watan Mayu, Mista Austin ya bukaci takwaransa da ya kira tsagaita bude wuta cikin gaggawa, ko da yake Amurka ba ta ambaci bukatar ba a wannan karon.
Hakan dai na zuwa ne bayan da shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya bayyana cewa watakila a shirye yake ya yi amfani da makaman nukiliya a Ukraine, da kuma gargadin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi.
Hukumomin Amurka da Birtaniya sun ce sun yi imanin cewa yiwuwar Mista Putin na aiwatar da wadannan barazanar babu tabbas.
Rikicin da ya yi tsami tsakanin Amurka da Rasha ya kara tabarbarewa tun bayan mamayar Ukraine.
Shugabannin kasashen biyu sun yi wata ganawa a tsakiyar shekarar 2021, wanda aka bayyana a matsayin wani mataki mai kyau na kyautata alaka.
Amma wannan ci gaban ya tsaya bayan da tashe-tashen hankula suka yi kamari a Ukraine.
Tun bayan mamayar dai babu wata tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen Amurka da Rasha.