Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi wa manema labarai bayani yau a nan birnin Beijing, kan ziyarar da wakilan kungiyar tarayyar kasashen Larabawa suke yi a jihar Xinjiang, ya ce, wakilan sun ganewa idanunsu yadda al’ummar jihar mai wadata ke rayuwa, inda suka bayyana matukar jin dadinsu kan nasarorin da aka samu a lasar Sin, musamman babbar nasara da aka samu a fannin yaki da talauci.
Wang Wenbin ya ce, ‘yan tawagar sun bayyana cewa, jihar Xinjiang da suka gani da idanunsu, ta sha bamban da yadda wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya suka bayyana, jihar Xinjiang tana da al’umma mai jituwa, da tattalin arziki mai wadata, jama’ar dukkan kabilu suna zaune lami lafiya, kana ana kara yin ayyuka daban-daban.
Ban da wannan kuma, musulman Xinjiang suna da ‘yancin gudanar da addini bisa doka, maganar cewa wai ana kisan kare dangi da zaluncin addini karya ce.
Daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan nan ne, tawagar kungiyar kasashen Larabawa ta kai ziyara jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, sama da jami’ai 30 daga kasashen Larabawa 16 da suka hada da Masar, Saudi Arabiya, da Aljeriya da sakatariyar kungiyar Larabawa sun halarci taron. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp