Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake saduwa a wannan mako a cikin shirin namu na ado da kwalliya.
Ya kamata uwargida ki san kalar turaran wuta, turaran wuta iri-iri ne:
Akwai turaran wuta na gida wanda shi za ki turara gida ne da shi kamar falo daki bandaki, shi irin wannan na gida ne, gida yana kamawa da kamshi idan kika saba wa gidanki yin turaran wuta gidanki zai kama kamshi duk randa bayi ba za ki ji gidanki akwai kamshi kamar kin yi turaran kamar a kalla sau uku a rana dake yanzu lokacin damuna ne ki yi da safe da rana sannan kuma da magriba.
Sai turaran wuta na jiki:
Shima wannan turaren wuta kalar shi daban yake sannan kuma kamshin shi daban yake, shi yadda ake amfani da shi uwargida idan kika fito a wanka kika shafa mai sai ki samu gaurashi ki zuba shi sannan ki ruhu da shi ki yishi kamar hayaki zai shiga jikinki sosai, sannan kuma fatarki za ta kama kamshi so sai duk inda kika wuce sai an ji wannan kamshi.
Sannan kuma kayan da za ki sa shima kin yi masa turaran wuta, shima turaran wuta na kaya daban yake yadda ake turaran wuta na kaya idan kika yi wanki da guga dama akwai abin da ake yi da shi idan kika je wajen masu turaren wuta za ki zame shi idan kika kawo shi za ki sa turaran cikin abun shi abun raga-raga ne, sannan sai ki dan bubbuda kayan haka sai ki shimfida akan abin da za ki iya shimfida kamar kala uku haka a kai harsai kin rufe ko ina raga kin ga babu ta inda kamshin ko hayakin yake fita ya zama duk jikin kaya yake shiga za ki tsaya ne saboda kar kamshi ya kare ya zama kauri.
Da zaran kin duba kin ga turaran ya kone sai ki yi sauri kwashe kayan saboda kar ya yi kauri kuma, kafin ki fara shimfida kayan idan kina da oil turaran za ki dan iya shafawa kayan saboda turaran wutar ya fi kama kaya idan kika shafa masa oil turaran, sannan kuma idan za ki iya kullum sanda za ki sa kayan sannan ne za ki yi masa turaran to wannan gaskiya kamshin sa ya fi tashi.
Sannan kina yi wa dorowarki ita ma saboda warin ruma.
Sannan akwai turaran lalle shima idan kika samu kwarar mai lalle har ma ‘yan Maiduguri idan aka sami lalle sai a miki turaren sa za ki ji yadda hannunki da kafarki za su dau kamshi.
Haba Uwargida Mace sai da kamshi idan kika maida hankali akan kamshi shi kade ya isheki ki mallaki maigida sai kinga yadda maigida zai na santi a kanki, ke kanki za ki ji kina san kanki kamshi ai rahma ne .