Shugaban kasar Timor-Leste, José Manuel Ramos-Horta, ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin tun daga ranar 28 har zuwa 31 ga watan Yulin bana, ziyarar da ta kasance karon farko da shugaban Timor-Leste ya kawo ziyara kasar Sin, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar jakadanci.
Yayin ziyararsa, wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya samu damar zantawa da shugaban Timor-Leste, wato José Manuel Ramos-Horta, inda ya bayyana ra’ayinsa kan dalilin da ya sa huldar kasashen biyu ta samu saurin ci gaba, yana mai cewa, Sin babbar kasa ce a duniya, wadda ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Asiya, kana kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya. A ’yan shekarun nan, kasar Sin ta samu ci gaba a fannoni da dama. Na farko, ta samu nasarori masu ban mamaki a fannin raya tattalin arziki, al’amarin da ya sa ta zama babbar kasa mai karfin tattalin arziki da hada-hadar kudi. Na biyu, karfin sojan kasar Sin ya bunkasa sosai, al’amarin da ya janyo kishi daga wasu kasashe, wadanda suka mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar takara, har ma wasu kasashen ke yunkurin taka birki ga ci gaban kasar Sin, amma irin wannan yunkuri nasu ya sha kaye tun a shekarun 1960 da 1970 na karnin da ya gabata.
Shugaba José Manuel Ramos-Horta ya kara da cewa, a wadannan shekaru, kasar Sin ba ta taba shiga duk wani yaki ba, ko yakin Afghanistan, ko na Yemen, ko na Iraki, ko na Libya, ko kuma rikicin Ukraine da har yanzu ake yi, sam kasar Sin ba ta shiga ciki ba. Sin kasa ce daya tak, da ba ta shiga cikin rikicin kasa da kasa ba, daga cikin zaunannun kasashe membobin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya. A sabili da haka, ya kamata kasar Timor-Leste ta kiyaye dangantakar kut da kut da irin wannan babbar kasa wato Sin. (Murtala Zhang)