Abdullahi Yakubu Dorayi, fitaccen dan jarida kuma wakilin jaridar Leadership, tsohon ma’aikacin jaridar Triumph ya rasu.
Labarin rasuwarsa ya karade gari a ranar Juma’a, 18 ga watan Agusta, 2023, wanda hakan ya bar jimami a kafafen yada labarai.
Abdullahi Yakubu Dorayi, wanda ya shahara da jajircewarsa ga aikin jarida da kuma alakarsa da kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), ya kasance mai matukar farin jini saboda gogewarsa da jajircewa wajen yada labarai.
Ya kasance wani jigo a aikin jarida wanda rike mukamai daban-daban, Dorayi.
Labarin rasuwar Abdullahi Yakubu Dorayi ya jefa alhini ga daukacin ‘yan jarida.
Abokan aikinsa sun koka game da rashinsa.
Mutane sun shiga mika ta’aziyyarsu ga iyalansa da ‘yan uwansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp