• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Kasar Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Daina Tsoma Bakin Soja Ba Bisa Ka’ida Ba A Syria

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

A yayin zaman taro na 51 na kwamitin kare hakkin dan-Adam, wakilin kasar Sin a kwamitin kare hakkin dan-Adam na MDD minista Jiang Duan ya yi Allah wadai da katsalandan din sojan da ya saba da doka da Amurka ta yi a kasar Syria.

Mr. Jiang Duan ya nuna cewa, matakin soja na Amurka ya keta muhimman hakkokin bil-adama na al’ummar Syria, don haka, ya bukaci kasar Amurka da ta gaggauta dakatar da take hakkin bil-Adam da take yi.

  • Matakan Soja Na Amurka Sun Jefa Wasu Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Matsala

Jiang Duan ya bayyana cewa, an shafe fiye da shekaru goma ana jinkirta batun kasar Syria, kuma har yanzu al’ummar kasar na fama da talauci da yaki. Kuma alhakin hakan ya rataya ne a wuyan Amurka da sauran kasashen yammacin duniya.

Kasar Amurka dai ta sha kaddamar da hare-haren soji a kasar Syria, lamarin da ya sabbaba hasarar rayukan fararen hula da matsugunai a Syria, tare da haddasa asarar dukiyoyi da ba za a iya misaltawa ba.

A watan da ya gabata ne sojojin Amurka suka kaddamar da wani sabon farmaki ta sama a gabashin kasar Syria, wanda ya ci gaba da keta hurumin kasar tare da kara ta’azzara wahalhalun da al’ummar Syria ke fama da shi.

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Bugu da kari, kasar Amurka ta kakkaba wa kasar Syria wasu matakai na tilastawa, wadanda suka saba doka, lamarin da ya sa al’ummar kasar wahalar samun zaman lafiya na yau da kullum, kuma matakan raya tattalin arziki da sake gina kasar, duk suna fuskantar matsaloli.

Har zuwa wannan lokaci, sojojin kasar Amurka ne ke da iko kan rijiyoyin man fetur, da iskar gas da sauran albarkatun kasar, inda suka mamaye manyan yankunan kasar da ake hako mai, tare da kwashe sama da kashi 80 cikin 100 na yawan man da ake hakowa a kasar, suna kuma fasa kwauri da lalata hatsin da kasar Syria ta adana, hakan ya keta ’yancin al’ummar kasar na samun abinci, da lafiya, da bunkasuwa, da sauran muhimman hakkoki na bil-Adama matuka.

Jiang Duan ya ce, rikicin kasar Syria ya nuna cewa, tsoma baki na kasashen waje, da tsokana, da matsin lamba, da sanya takunkumai, ko kadan ba za su taimaka wajen warware matsalar ba. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Next Post
Wang Yi Ya Zanta Da Sakataren Wajen Amurka

Wang Yi Ya Zanta Da Sakataren Wajen Amurka

LABARAI MASU NASABA

Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

November 8, 2025
NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.