A jiya Talata ne wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya cewa ya kamata su kara hakuri da yadda harkokin siyasa ke gudana a Sudan ta Kudu, kasa mafi karancin shekaru a duniya.
Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya kara kira ta musamman ga kasashen duniya da su mutunta ‘yancin kasar Sudan ta Kudu da ikon mallakarta, da kaucewa matsin lamba da tsoma baki daga waje.
Ya kuma yi kira ga asusun ba da lamuni na duniya IMF da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa da su ci gaba da kara tallafin kudi ga Sudan ta Kudu.
Sudan ta Kudu ta sha nanata cewa takunkumin makamai da aka kakkaba mata na da mummunan tasiri wajen tabbatar da tsaron kasa, in ji Dai, ya kuma kara da cewa kasashen yankin sun sha yin kira da a dage takunkumin da ba su dace ba kan Sudan ta Kudu. (Yahaya)