Wakilin kasar Sin ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, hukumar shiga tsakani ta duniya (IOMed) za ta kasance babbar hukuma mai aiki a tsakanin gwamnatocin kasashen duniya wajen taimaka wa sulhunta takaddamar kasa da kasa ta hanyar shiga tsakani.
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Vienna Li Song, ya bayyana hakan a yayin wata liyafar karfafa yayata hukumar ta IOMed, da aka gudanar a yayin zaman taro na 58 na kwamitin majalisar dinkin duniya kan dokar cinikayya ta kasa da kasa (UNCITRAL).
Yayin da yake lura da cewa, kundin tsarin mulkin MDD ya bayyana karara cewa, yin sulhu na daya daga cikin hanyoyin da aka fi so wajen warware takaddamar kasa da kasa cikin lumana, Li ya ce IOMed za ta kasance halastacciyar hukuma mai aiki a tsakanin gwamnatocin duniya ta farko da ta himmatu wajen warware takaddamar kasa da kasa ta hanyar shiga tsakani.
IOMed dai wata kyakkyawar muhimmiyar kafa ce ta jama’ar duniya da kasar Sin ta samar tare da sauran kasashe masu ra’ayi iri daya, don cimma yanayin ci gaba na zamani da kuma bukatar shiga tsakani a bangaren kasa da kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp