Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila, da ta dage takunkumin shigar da kayan agajin jin kai cikin zirin Gaza, kana ta dakatar da amfani da batun agajin jin kai a Gaza, a matsayin hanyar cimma bukatar kashin kai, duba da yadda yanayin da fararen hula ke ciki a birnin ke matukar kara ta’azza. Fu Cong, wanda ya yi kiran a jiya Talata, cikin tsokacin da ya yi ga zaman kwamitin tsaron MDDr, don gane da karancin abinci a Gaza, ya ce bai kamata a siyasantar da wannan batu ba, kana bai dace a mayar da yunwa makami ba. Ya ce wannan sanannen abu ne a dokar jin kai ta kasa da kasa. To sai dai kuma Fu Cong, ya bayyana takaici, game da rikicin na Gaza, wanda a yanzu ya shiga wata na 13, ake hana fararen hula samun kayayyakin biyan bukatun yau da kullum, ake kuma keta dukkanin dokokin jin kai ba kakkautawa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)