Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga sassan da ba sa ga maciji da juna a kasar Somaliya, da su kara azamar karfafa tattaunawa, da dunkulewa wuri guda, kana su nacewa warware sabani ta hanyar gudanar da shawarwari.
Dai Bing, wanda ya yi kiran a jiya Alhamis, yayin zaman kwamitin tsaron MDD game da kasar ta Somaliya, ya ce a shekarun baya bayan nan, Somaliya ta cimma manyan nasarori a fannonin sake gina kasa, da wanzar da zaman lafiya da tsaro, kuma tawagogin MDD da na kungiyar tarayyar Afirka ta AU dake kasar sun kai ga shiga lokaci na kyakkyawan sauyi a kasar. Don haka a wannan lokaci mai muhimmanci, bai dace a sassauta tallafin da sassan kasa da kasa ke baiwa Somaliyar ba.
Jami’in na Sin ya kuma jaddada wasu muhimman batutuwa uku, wato bukatar wanzar da yanayin siyasa bisa daidaito, da karfafa tushen sauya akala zuwa yanayin tsaro mai karko, da ingiza ci gaban ayyukan rundunar MDD mai aiki a Somaliya ko UNSOM bisa tsari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp