Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasa Switzerland Chen Xu ya yi jawabi a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 58 kan batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, inda ya yi bayani game da tunanin Sin kan kare hakkin dan Adam da kin amincewa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam.
Chen Xu ya yi nuni da cewa, ana bukatar bin ra’ayin bangarori daban daban da tunanin kare hakkin dan Adam da yin hadin gwiwa mai amfani don sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam. Wasu kasashe sun yi amfani da dalilin kare hakkin dan Adam wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe, da yin amfani da ma’auni biyu, da tada rikice-rikice, da kuma kakabawa wasu takunkumi daga bangare daya. Wadannan kasashe sun kau da kai daga yanayinsu na keta hakkin dan Adam, da maida kansu a matsayin alkalan kare hakkin dan Adam, da zargin wasu kasashe kan yanayin kare hakkin dan Adam, sun kawo illa ga tsarin kare hakkin dan Adam na MDD.
Chen Xu ya kara da cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan tunanin kare hakkin dan Adam bisa tushen kyautatawa jama’a, da kiyaye tabbatar da moriyar jama’a. Kasar Sin tana girmama jama’ar sauran kasashe wajen zabar hanyar raya hakkin dan Adam da kansu, da kuma samar da gudummawa wajen raya tsarin siyasa na duk dan Adam baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp