Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce ya kamata kasashen duniya su kiyaye ka’idar “warware al’amuran Afirka ta hanyar Afirka”, da kauce wa matsin lamba mai karfi, da kuma karfafawa bangarori daban daban masu ruwa da tsaki gwiwa, wajen kawar da bambance-bambance ta hanyar tattaunawa, da goyon bayan kasashen yankin wajen lalubo hanyoyin ci gaba da suka dace da yanayin su.
Geng Shuang ya bayyana haka ne a gun budadden taro na kwamitin sulhu na MDD game da yammacin Afirka da yankin Sahel da aka yi jiya Jumma’a.
- Zakarun Gasar Olympics 42 Za Su Jagoranci Tawagar Kasar Sin A Gasar Olympics Ta Paris
- Ba Zan Taba Mantawa Da Zamowata Gwarzuwar Banki Sau Biyu A Jere Ba – Fatima Gana
A cewarsa, kasar Sin ta yi maraba da taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da aka yi kwanan nan, da kuma sake zabar shugaban Najeriya a matsayin shugaban riko na kungiyar ECOWAS. Haka kuma, tana sa ran kungiyar ECOWAS za ta ci gaba da hada kai da kasashen yankin, da kuma taka rawa wajen inganta hadin kai, da tabbatar da zaman lafiya da ma inganta ci gaban yankin.
Kaza lika, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana yabawa kokarin ECOWAS da kasashen yankin wajen yaki da ta’addanci, kuma tana matukar damuwa da yadda yanayin ta’addanci ya ci gaba da tsananta a yankin. Ya ce kasar Sin ta yi maraba da yadda kungiyar ECOWAS ta inganta aikin gina rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta’addanci, da kuma sanar da kafa cibiyar yaki da ta’addanci a Najeriya da aka yi a babban taron yaki da ta’addanci na kasashen Afirka, kana da goyon bayan ECOWAS don ta ci gaba da taka rawar gani wajen yaki da ta’addanci a yankin da kuma karfafa hadin gwiwa baki daya a shawarwarin yaki da ta’addanci daban-daban na yankin. (Bilkisu Xin)