Yau Talata 2 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da manema labarai, bayan ya halarci taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kai ta birnin Shanghai ko SCO, da kuma ziyarar sa a wasu sassa na nahiyar tsakiyar Asiya, inda ya bayyana matsayin da Sin take dauka kan batun yankin Taiwan.
Wang Yi ya yi nuni da cewa, manufar “kasar Sin daya tak a duniya” na samun amincewa daga kasashen duniya, kuma tsari ne mai tushe ga kasar Sin, na daidaita huldarta da kasashen waje, kuma muradi mai tushe na kasar Sin, kuma ba wanda zai ware yankin Taiwan daga babban yankin Sin ba.
Wang ya jaddada cewa, Amurka ta ci amana kan batun yankin Taiwan, matakin da zai lalata kimarta a duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp