Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana a jiya Lahadi yayin ziyarar da ya kai kasar Bangaladesh cewa, kasar Amurka ta yi kuskure a bangarori uku, dangane da ziyarar gangancin da shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na kasar Sin.
Wang Yi ya bayyana haka ne, a matsayin mayar da martani ga yanayin da ake ciki na baya-bayan nan da yadda bangaren Amurka yake jujjuya maganar.
Da farko, Wang ya ce, bangaren Amurka ya yi katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin. Yana mai cewa, duk da sanarwa da kuma gargadin da kasar Sin ta sha yi, amma Amurka ta yi gaban kanta, ta kuma shirya wa jami’a mai matsayi na uku a gwamnatin Amurka don kai wannan ziyara zuwa yankin Taiwan na kasar Sin.
Na biyu, ya ce, Amurka ta hada kai tare da goyon bayan masu neman “’yancin kan Taiwan”, don haka, wajibi ne kowace kasa ta kiyaye hadin kan kasa, kuma bai kamata ta taba bari ‘yan aware su rika nuna halin ko-in-kula ba.
Na uku, da gangan Pelosi ta yi wa zaman lafiya zagon kasa a mashigin tekun Taiwan. Kuma kamar yadda kowa ya sani, a ko da yaushe, Amurka ce take fara haifar da matsala, sannan kuma ta yi amfani da ita wajen cimma manufofinta bisa dabarun da ta tsara.
Wang ya ce, kasar Sin ta yaba da fahimtar juna da goyon bayan da kasashe daban-daban suka nuna mata.
Yana mai cewa, yayin da ake gudanar da ayyukan cin zarafi na kashin kai daga lokaci zuwa lokaci, ya kamata kasashen duniya su cimma matsaya karara, da yin magana da babbar murya, ta yadda za su kiyaye muhimman ka’idojin dangantakar kasa da kasa, da dokokin kasa da kasa, da kiyaye ’yanci da muradun dukkan kasashe masu tasowa. (Ibrahim Yaya)