Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin.
Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida.
Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci, da nuna adawa da kariyar cinikayya, da kare daidaito da adalci a duniya.
Yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Uzbekistan Bakhtiyor Saidov, duk dai a wannan ranar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashe masu ra’ayi iri daya, wajen kiyaye damawa da kowa da kowa, da kare daidaito da adalci, da kuma nuna adawa da kariyar cinikayya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp